A kaf Gwamnatin Buhari, babu wanda ya san harkar tattali – Atiku

A kaf Gwamnatin Buhari, babu wanda ya san harkar tattali – Atiku

Mun samu labari cewa ‘Dan takarar Jam’iyyar hamayya ta PDP, Atiku Abubakar, yayi ikirarin cewa babu wani mutum guda da za a nuna da yake ilmin tattalin arzikin a cikin Gwamnatin Shugaban kasa Buhari.

A kaf Gwamnatin Buhari, babu wanda ya san harkar tattali – Atiku

Atiku yace Gwamnatin Buhari ta jahilici lamarin tattalin arziki
Source: Facebook

Atiku Abubakar yayi wannan jawabi ne a farkon makon nan lokacin da ya gana da gungun wasu Matasa a cikin Garin Legas. Atiku ya bayyana cewa Mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo ba Masanin harkar tattalin arziki bane.

Atiku yace babban aikin Mataimakin Shugaban kasa shi ne ya rika lura da tattalin arzikin kasa. ‘Dan takarar na PDP yace Osinbajo, Farfesan shari’a ne ba na harkar tattali ba don haka kuwa bai da ilmi a lamarin da ya shafi tattali.

KU KARANTA: Buhari ya gaza cika alkawuran da ya yiwa 'yan Najeriya - Atiku

Atiku Abubakar ya bayyana cewa Gwamnatin APC ta gaza shawo kan tattalin arzikin Najeriya inda yace a cikin mukarraban Shugaba Buhari, babu wani wanda ya karanci ilmin harkar tattalin arziki da har za a iya kai kasar nan ga ci.

A cewar ‘Dan takaran Shugaban kasar, idan har Buhari ya zarce, abubuwa za su kara sukurkucewa a Najeriya ta fannin tattalin arzikin kasa. Atiku yace rayuwar al’ummar Najeriya ta dogara ne da yadda aka rike tattalin kasar nan.

Alhaji Atiku ya tunawa jama’a lokacin da ya rike mukamin Mataimakin Shugaban kasa a lokacin Gwamnatin Obasanjo, inda yace sun kawo tsare-tsare inda har ta kai tattalin arzikin Najeriya ya bunkasa kwarai a lokacin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel