Gwamnatin Najeriya na da halin biyan N30,000 mafi karancin albashi - Oshiomhole

Gwamnatin Najeriya na da halin biyan N30,000 mafi karancin albashi - Oshiomhole

Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Kwamared Adams Oshiomhole, ya bayyana goyon bayan sa tukuru ga kungiyar kwadago ta kasa, dangane da kudirinta gami da fafutikar tabbatar da N30, 000 a matsayin sabon mafi karancin albashin ma'aikatan kasar nan.

Oshiomhole ya jaddada cewa, kasancewarsa mamba na kungiyar gwamnonin Najeriya yayin da yake kan karagar mulki ta kujerar gwamnan jihar Edo, ya shaidawa takwarorin sa matsayarsa ta rashin tarayyarsa da su inda yake goyon bayan kudirin kungiyar kwadago akan mafi karancin albashin ma'aikata.

Shugaban jam'iyyar ya bayyana hakan ga manema labarai yayin halartar bikin taya murna na Ayuba Wabba, dangane da zaben sa a matsayin shugaban kungiyar kwadago ta kasa da kasa da Safiyanu Muhammad, Sakataren cibiyar sufuri ta kasa da kasa reshen Afirka.

Gwamnatin Najeriya na da halin biyan N30,000 mafi karancin albashi - Oshiomhole

Gwamnatin Najeriya na da halin biyan N30,000 mafi karancin albashi - Oshiomhole
Source: Depositphotos

Oshiomhole yake cewa, matsayar da yake kai tun fil azal, a halin yanzu ba za ta sauya ba duk da kasancewar sa shugaban jam'iyyar APC na kasa da kudirin sa ya sabawa wasu gwamnoni na jam'iyyar.

KARANTA KUMA: Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga dadi sun halbe Alex Badeh har lahira

Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, shugaban jam'iyyar ya ci gaba da cewa, wannan kudiri ba ya da wata alaka ta kusa ko ta nesa da siyasa, illa iyaka nasaba mai karfin gaske inganta jin dadin ma'aikata domin ci gaban kasa.

Kazalika jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa, kawar da yunwa, fatara da kuma rashin aikin yi a kasar nan ita kadai ce hanyar kawo karshen ta'addancin kungiyar ta'adda ta Boko Haram.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel