Ta'addancin Makiyaya zai kara ta'azzara muddin Buhari ya yi nasara a zaben 2019 - Atiku

Ta'addancin Makiyaya zai kara ta'azzara muddin Buhari ya yi nasara a zaben 2019 - Atiku

Dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya gargadi al'ummar Najeriya dangane da wani mummunan lamari da ba zai yanke ba cikin kasar nan muddin shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi nasara a zaben 2019.

A jiya Talata, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa, ta'addanci makiyaya na kashe-kashe da zubar jinin al'umma a Najeriya ba zai yanke ba muddin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi nasara a zaben 2019.

Atiku ya bayyana hakan yayin mayar da martani dangane da binciken kungiyar Amnesty International da ta bayyana cewa, aukuwar rikicin makiyaya da manoma ta salwantar da rayukan kimanin Mutane 3, 641 cikin tsawon shekaru uku da suka gabata.

Babban hadimi na musamman mai magana da yawun tsohon Mataimakin shugaban kasar, Mista Phrank Shu'aibu, shine ya bayar da shaidar hakan cikin wata sanarwa a jiya Talata yayin ganawa da manema labarai.

Ta'addancin Makiyaya zai kara ta'azzara muddin Buhari ya yi nasara a zaben 2019 - Atiku

Ta'addancin Makiyaya zai kara ta'azzara muddin Buhari ya yi nasara a zaben 2019 - Atiku
Source: Twitter

Mista Phrank yake cewa, muddin al'ummar Najeriya ba su mike tsaye ba wajen fatattakar gwamnatin jam'iyyar APC, to kuwa sai dai abinda aka gani dangane da kashe-kashen makiyaya da ba zai yanke ba illa iyaka ta'azzarasa da ka iya haddasa mummunan rikici na kabilancin a fadin kasar nan.

Ya ci gaba da cewa, binciken cibiyar Amnesty International ya tabbatar da gazawar gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Shugaban kasa Buhari ta fuskar rashin samar da kariya da tsare rayukan al'umma.

Atiku ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya a halin yanzu ta gaza ta fuskar cancantar kawo karshen kalubalai da barazanar tsaro da ke ci gaba da addabar kasar nan, inda ta yi sanadiyar salwantar rayukan dubban Mutane yayin da wasu suka nakasa.

KARANTA KUMA: Amaryar sanata Yarima da ya aura tana karama ta girma, hoto

Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, Atiku ya kara da cewa, kashe-kashe gami da zubar da jinin al'umma ya taka muhimmiyar rawa wajen fatattakar masu hannayen jarin kasashen ketare daga kasar Najeriya.

A yayin haka jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, shugaban kasa Buhari na mika kokon bararsa ga kungiyar malaman jami'o'in kasar nan ta ASUU, akan ta janye yajin aikin da afka tun a watan Nuwamba da ya gabata domin dalibai su koma fagen fama na karatuttukan su.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel