Gwamnati ta sanya makurar lokacin gudanar sana'ar Acaba a jihar Ondo

Gwamnati ta sanya makurar lokacin gudanar sana'ar Acaba a jihar Ondo

Mun samu rahoton cewa, a ranar Talatar da ta gabata, gwamnatin jihar Ondo da ke Kudancin Najeriya, ta bayar da sanarwar shimfidar wata sabuwar doka ta talala ga ma su sana'ar Acaba watau Kabu-Kabu na babura a fadin jihar.

Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, gwamnatin jihar karkashin jagorancin gwamna Rotimi Akeredolu, ta shimfida dokar takunkumi akan gudanar da harkokin sana'ar Acaba a fadin jihar.

Gwamnatin ta kayyade dokar haramtawa 'yan Acaba cin kasuwarsu bayan karfe 10.00 na daren kowace rana cikin kananan hukumomi 18 da ke fadin jihar.

Kwamishinan yada labarai na jihar, Mista Yemi Owolabi, shine ya bayyana hakan yayin ganawarsa da manema a yammacin jiya Talata cikin babban birnin jihar na Akure.

Gwamnati ta sanya makurar lokacin gudanar sana'ar Acaba a jihar Ondo

Gwamnati ta sanya makurar lokacin gudanar sana'ar Acaba a jihar Ondo
Source: Depositphotos

Owolabi ya bayyana cewa, gwamnatin jihar karkashin jagorancin Gwamna Akeredolu, ta yi wannan hobbasa domin tsarkake jihar daga miyagun laifuka da kuma tabbatar da da'a da kiyaye doka.

Kamar yadda dokar ta shar'anta, an haramtawa kowane dan kabu-kabu daukar fasinja bayan karfe 10.00 na daren kowace rana. Kazalika dokar ta tursasawa kowane dan Acaba gabatar da takardun shaidar mallakin baburan su na sana'a a duk sa'ilin da hukuma ta bukata.

Sai dai Kwamishinan ya jaddada cewa, wannan sabuwar doka ta takaita ne kadai akan masu baburan haya. Ya ce ba bu wannan doka akan mamallakan baburan hawa ma su zaman kansu domin bukatun kawunan su wajen fita aiki ko kuma biyan bukatu na gaggawa.

KARANTA KUMA: Karancin maza: ‘Yan mata sun kai samarin jihar kara wajen mai unguwa

Mista Owolabi ya nemi daukacin al'ummar jihar musamman masu sana'ar Acaba wajen tankado keyar miyagun mutane ma su aikata barna a fadin jihar.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, wasu shu'uman Mata biyu da suka shahara da ta'addancin garkuwa da Mutane sun shiga hannun hukumar 'yan sanda a jihar Kaduna da ke Arewacin Najeriya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel