PDP na zargin wani sabon tuggu na tsige Saraki

PDP na zargin wani sabon tuggu na tsige Saraki

Da sanadin shafin jaridar Vanguard mun samu rahoton cewa, a halin yanzu jam'iyyar adawa ta PDP na zargin wata sabuwar kitimurmura ta shugaban kasa Muhammadu Buhari, da kuma jam'iyyar sa ta APC, akan yiwa shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki, sakiyar da ba bu ruwa.

Jam'iyyar adawa ta PDP ta bayyana damuwa zargin ta kan wani sabon tuggu na ribatar hukumar 'yan sanda da kuma ta DSS wajen tsige shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki, ta karfi da yaji.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, jam'iyyar PDP ta bayyana fargabar ta gami da zargin wata kitimurmura ta tsige Saraki daga kan kujerar sa ta shugabancin majalisar dattawan kasar nan, da a halin yanzu ya kasance shugaban kungiyar yakin neman zaben kujerar shugaban kasa na jam'iyyar.

Cikin wata sanarwa da san hannun Mista Kola Ologbondiya a jiya Talata, kakakin jam'iyyar ya yi tir da wannan lamari da ya misalta a matsayin yiwa doka karan tsaye gami da cin mutunci keta hakkin dan Adam da gwamnatin jam'iyyar APC ta dabbaka a fadin kasar nan.

PDP na zargin wani sabon tuggu na tsige Saraki

PDP na zargin wani sabon tuggu na tsige Saraki
Source: Depositphotos

Kakakin jam'iyyar ya bayyana cewa, manufar wannan kitimurmura ta tsige Saraki daga kujerar sa ta mulki ta bayu ne kadai domin kawo tangarda bisa ga nasarorin da jam'iyyar PDP ke ci gaba da samu tun gabanin kaddamar da yakin ta na neman zabe da ke hasashen nasararta a babban zaben kasa na badi.

KARANTA KUMA: Wasu shu'uman mata 2 da ke garkuwa da mutane a Kaduna sun shiga hannu

Cikin sanarwar kakakin jam'iyyar, Misa Ologbondiyan ya bayyana cewa, wani bigire na wannan tuggu bai wuci amfani da hukumomin tsaro ba musamman jami'an 'yan sanda da kuma na DSS, wajen kagar laifuka akan Saraki domin tarwatsa aniyya da kudurin yakin neman zabe na jam'iyyar PDP.

A yayin haka jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, wata kungiyar hadin kai ta Najeriya, Coalition of Nigeria, CN, ta bayyana cewa lallai jam'iyyar PDP na kulla tuggu na shirya magudin zabe domin samun nasara da kowane hali.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel