Na shirya gamuwa da mahalicci na - Buhari

Na shirya gamuwa da mahalicci na - Buhari

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu yace shi fa ya shirya haduwa da mahaliccin sa cikin salama da aminci domin yasan bai cuci kowa ba kuma bai saci kudin talakawa ba balle ya tara dukiyar da ta wuce misali.

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a cikin wani faifan bidiyon da wata mai goyon bayan sa ta wallafa a shafin ta na dandalin sadarwar zamani na Facebook mai suna Maryam Shetty a kwanakin baya.

Na shirya gamuwa da mahalicci na - Buhari

Na shirya gamuwa da mahalicci na - Buhari
Source: Twitter

KU KARANTA: Karancin maza: 'Yan mata sun kai karar mazan unguwar su a Kano

Legit.ng Hausa ta samu cewa a cikin bidiyon, an tsinkayi shugaban kasar yana cewa shi fa tara abun duniya bai dame shi ba domin sam bai yadda da ya saci ko da sisin kobon talakawa ba.

Ya kara da cewa a irin rayuwar sa da yake yi yanzu, yana da yakinin cewa ya shirya haduwa da mahaliccin sa cikin salama da aminci.

Ga dai bidiyon nan:

A wani labarin kuma, Mukaddashin hukumar nan dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) a takaice, Ibrahim Magu ya ce shi yaji dadi sosai da majalisar dattawa ta ki amincewa da shi a matsayin tabbataccin shugaban hukumar ta EFCC.

Ibrahim Magu ya yi wannan ikirarin ne a wata kotu, jihar Legas gaban alkali lokacin da yake bayar da shaida akan wata karar da ya shigar yana kalubalantar wata jarida da yace tayi masa kazafi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel