Buhari ya ki sanya hannu kan dokar hukumar NBC, ya bayar da dalili

Buhari ya ki sanya hannu kan dokar hukumar NBC, ya bayar da dalili

Shugaba Muhammadu Buhari ya ki amincewa da wani kudirin doka da ke naman yin garambawul ga dokar da ta kafa hukumar watsa labarai na kasa (NBC).

A baya, majalisar tarayya ta amince da kudin doka da ke neman yin garambawul ga hukumar ta NBC kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Shugaba Buhari ya bayyana rashin amincewarsa da yiwa dokar gyara a cikin wata wasika da ya aike wa shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki.

Buhari ya ki saka hannu a akan wata doka da majalisa da aike masa, ya fadi da dalili

Buhari ya ki saka hannu a akan wata doka da majalisa da aike masa, ya fadi da dalili
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Sojoji sun ragargaji 'yan ta'addar Zamfara, hotunan wadanda suka mutu

Shugaban majalisar ya karanto wasikar a zauren majalisar a yau Talata.

A cikin wasikar shugaban kasar ya yi bayyanin cewa ya ki amincewa da kudirin yiwa dokar garabawul ne saboda an cire wasu sakin layi na 21(U) wadda suke dauke da muhimman bayanai da ya bawa hukumar ikon gudanar da wasu ayyuka wanda babu shi a sabon dokar.

"Kamar yadda sashi na 58(4) na kudin tsarin mulkin Najeriya ya bayar da dama, ina son in sanar da majalisa rashin amincewar shugaban kasa game da kundin dokar Hukumar watsa labarai na kasa na 2018 a yau 26 ga watan Nuwamba.

"Na ki amincewa da kundin dokar ne saboda an cire sakin layi na 21(U) wanda ke dauke da muhimman bayanai da suka bawa hukumar ikon aikata wasu abubuwa da ba a tanadar da su a sabuwar kudirin ba."

Shugaban kasar ya shawarci majalisa tayi bita tare da yin gyra cikin kundin tsarin mulkin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel