Ta bayyana: Atiku ya dauki nauyin wanda ya taimakawa Trump wajen magudin zaben Amurka, ya kawo shi Najeriya

Ta bayyana: Atiku ya dauki nauyin wanda ya taimakawa Trump wajen magudin zaben Amurka, ya kawo shi Najeriya

Yayinda ake cigaba da zarge-zarge tsakanin jam'iyyun adawa kan zaben 2019, wata kungiyar fafutuka mai suna Coalition for Nigeria CN ta ce lallai fa akwai wani tuggu da jam'iyyar PDP ke shiryawa na magudin zabe domin samun nasara.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a wata hira da manema labarai ranan Talata a birnin Legas. Game da cewar Sakataren kungiyar, Mr Dipo Samuel, dan takaran jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya saki kudade domin aiwatar da wannan tuggu.

Yace: "Lokacin da dan takaran PDP, Atiku Abubakar, ya dauki wani kwararren dan Amurka, Brian Ballard, aiki domin zabe, mun bayyana damuwarmu saboda wannan mutumi ne ya taimakawa shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ta hanyar amfani da masana daga kasar Rasha wajen magudin zaben Amurka har ya smau nasara. A yanzu haka an shigo da shi Najeriya."

"Ya bayyana yanzu cewa ba wani aiki Brian Ballard ya zo yi Najeriya ba illa ya shirya tuggu."

"A cikin shirye-shiryen Ballard, mun samu labarin cewa anyi wasu canje-canje cikin hukumar INEC inda aka sanya wadansu a wurare da zai musu saukin canje-canje cikin yanar gizon hukumar."

"Wajibi ne hukumar INEC ta tashi tsaye domin tabbatar da tsaron kayayyakin aikinta da kuma karesu da harin wadannan mutane. Kana, wajibi ne hukumar INEC ta tabbatar da cewa ta duba wadanda aka sanya a wasu wurare na Allah ne. Bayan haka, INEC ta fito ta bayyanawa Najeriya cewa yan kasan Rasha ba zasu kawo rikici kamar yadda suka kai kasar Amurka ba."

Zaku tuna cewa jam'iyyar APC ta kai kukan labarin da ta samu cewa jam'iyyar PDP na shirin amfani da yan kasar Rasha wajen magudin zaben 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel