Kotun daukaka kara ta wanke manyan Alkalan kasar nan daga zargin cin hanci da gwamnatin Buhari ke musu

Kotun daukaka kara ta wanke manyan Alkalan kasar nan daga zargin cin hanci da gwamnatin Buhari ke musu

- Kotun daukaka kara ta soke karar da Gwamnatin tarayya ta shigar

- Karar na kalubalantar sakin mai shari'a Ademola, matar shi da Joe Agi akan amsa tambayoyin zargin damfara

- Mai shari'a Ige yace dalilan daukaka karar basu da tushe balle makama

Kotun daukaka kara ta wanke manyan Alkalan kasar nan daga zargin cin hanci da gwamnatin Buhari ke musu

Kotun daukaka kara ta wanke manyan Alkalan kasar nan daga zargin cin hanci da gwamnatin Buhari ke musu
Source: UGC

Kotun daukaka kara a ranar litinin ta soke daukaka karar da Gwamnatin tarayya tayi tana kalubalantar sakin mai shari'a Adeniyi Ademola, matar shi Olubowale da Joe Agi daga amsa tambayoyin zargin damfara.

Ofishin dillancin labarai ya ruwaito a kwanaki cewa a ranar 5 ga watan Afirilu ne babban kotun tarayya dake Abuja ta kori duk laifuka 18.

DUBA WANNAN: Tsage gaskiya: Aikin waye kawo jirgin kasa daga Abuja zuwa jihohi?

Mai shari'a Olabisi Ige yace duk dalilan da masu daukaka karar suka mika ga kotun daukaka basu da makama. Mai shari'ar yace ba hurumin kotun bane tayi gatsali ga hukuncin babbar kotun ba tare da dalilai masu kyau ba.

Kamar yanda yace dalilan da masu daukaka karar suka gabatar basu da makama. Yace dalilan basu kai abinda zai sa a dawo da mutane ukun gaban kuliya ba.

Mai shari'a Ige yace wasu masu bada shaidar masu karar a gaban kotun basu san dalilin binciken ba.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa.

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel