Buhari zai je Kano ranar Alhamis kuma ana sa ran zai kunyata Ganduje

Buhari zai je Kano ranar Alhamis kuma ana sa ran zai kunyata Ganduje

Ana sa ran Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari zai je makarantar horas da 'yan sanda dake a garin Wudil ta jihar Kano a ranar Alhamis din nan mai zuwa domin halartar bikin yaye sabbin daliban da makarantar ta horas tare da bayar da lambobin yabo ga zakakurai a cikin su.

Sai dai kuma ana tunanin zai kunyata Gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje domin kuwa ana sa ran ba zai je gidan gwamnatin jihar ba a ranar duk kuwa da kasancewar su a jam'iyya daya kuma al'ada ta gaji haka.

Buhari zai je Kano ranar Alhamis kuma ana sa ran zai kunyata Ganduje

Buhari zai je Kano ranar Alhamis kuma ana sa ran zai kunyata Ganduje
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Rikici tsakanin yan sanda da masu hakar ma'adanai ya barke a Taraba

Legit.ng Hausa ta samu daga majiyar mu ta DailyNigerian cewa wata majiya daga fadar shugaban kasar ta bayyana cewa zargin karbar cin hancin dalolin da ake yiwa gwamnan ne babban dalilin kauracewar da shugaban kasar zai yi wa gwamnan.

A wani labarin kuma, Karamin ministan albarkatun man fetur na kasar Najeriya Mista Ibe Kachikwu ya bayyana cewa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari har yanzu bata zuba ko da kwandalar ta ba a cikin matatun man fetur din kasar nan.

A cewar Ministan, wannan ko shakka babu wata nasara ce da gwamnatin ta samu amma wadda al'ummar kasa ba su maida hankali a kai ba musamman idan aka yi la'akari da gwamnatocin ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel