Ministan Kasar Australia ya yi murabus kan dambarwar neman Mata

Ministan Kasar Australia ya yi murabus kan dambarwar neman Mata

- Wani karamin Minista a kasar Australiya ya yi murabus daga mukamin sa kan aikata abin kunya

- Minista ya ce zai yi hannun riga daga dukkanin harkokin siyasa a shekarar 2019

- Andrew Broad ya bai wa dukkanin masoya da abokanan huldarsa hakurin kan bata ma su suna

A yau Talata mun samu rahoton cewa, wani Ministan gwamnatin kasar Australia, Andrew Broad, ya yi murabus daga mukamin sa biyo bayan dambarwa ta zargin sa da aikata babban laifi na abin kunya wajen bibiyar 'yan Mata Matasa.

Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, Ministan ya kuma jaddada alwashin sa na yin hannun riga da duk wata harka ta siyasa a shekarar 2019 mai gabatowa.

Mista Broad ya yi murabus daga kujerar sa ta karamin Minista Mataimakin Firai Ministan kasar, Michael McCormack a jiya Litinin, biyo bayan tonan sililin da wata mujallar ta yi a kansa dangane da abin kunyar da yake aiktawa.

Ministan Kasar Australia ya yi murabus kan dambarwar neman Mata

Ministan Kasar Australia ya yi murabus kan dambarwar neman Mata
Source: UGC

Mujallar ta Tabloid ta zayyana cewa, Mista Broad duk da kasancewar sa Magidanci, yana amfani da wani shafin masoya na yanar gizo wajen bibiyar 'yan Mata Matasa a lokacin da yake tafiye-tafiyensa na aiki.

Cikin gabatar da shaidar ta, Mujallar ta yi ikirarin yadda Mista Broad ya kwashe dare da wata Matashiya da ya girma da kimanin shekaru 20 a birnin Hong Kong bayan saduwarsa a shafin na Masoya a watan Nuwamba da ya gabata.

KARANTA KUMA: Gwamnati ta dauki Mata 1500 aikin karantarwa a jihar Kano

Da yake bayyana nadamarsa gami da da na sani, Mista Broad ya nemi afuwar dukkanin abokanan huldarsa, masoya, 'yan uwa da kuma iyalansa dangane da wannan abin kunya da ya aikata kamar yadda bayar shaida cikin wata sanarwa.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayar da tabbacin samun zaman lafiya a fadin kasar muddin ya lashe kujerar shugaban kasa a zaben 2019.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel