Dalilai 6 da suka sanya ma'aikatan majalisar tarayya shiga yajin

Dalilai 6 da suka sanya ma'aikatan majalisar tarayya shiga yajin

Tun a ranar Lahadi ne kungiyar ma'aikatan majalisar tarayya (PASSAN) ta fitar da sanarwar cewar zata shiga yajin aikin gargadi daga ranar Litinin zuwa Alhamis domin neman wasu hakkokinsu da suka ce sun makale a wurin shugabanninsu.

Tun kafin wannan sanarwa, maikatan majalisar sun gudanar da wata zanga-zanga a kofar shiga majalisar a cikin makon jiya da ta kai ga hana mambobin majalisar gudanar da zaman majalisa.

Ko a yau, Talata, ma'aikatan majalisar sun sake gudanar da wata zanga-zangar duk da suna cikin yanayin yajin aiki.

Dalilai 6 da suka sanya ma'aikatan majalisar tarayya shiga yajin

Dalilai 6 da suka sanya ma'aikatan majalisar tarayya shiga yajin
Source: UGC

Da yake magana da wakilin jaridar legit.ng, shugaban kungiyar PASSAN, Bala Hadi, ya ce kungiyar ta shiga yajin gargadi ne da zai kare ranar Alhamis.

Ya kara da cewar muddin shugabannin majalisar basu dauki wani mataki ba bayan yajin aikin gargadin, zasu dauki matakin da ya fi wannan tsauri.

DUBA WANNAN: PDP: Kotu ta kwace takarar gwamna daga hannun Sanata Buruji

Ga jerin bukatun kungiyar kamar yadda Hadi ya bayyana.

1. Muna neman hakkokinmu da kuma inganta yanayin aikinmu a majalisa

2. A sakar mana dukkan wasikun karin girma da suka makale, har yanzu shiru.

3. A sake kafa hukumar kula da ma'aikatan majalisa tunda wa'adin wacce aka kafa a baya ya kare tun watan Yuli

4. Bawa ma'aikatan majalisar tarayya horo a kan lokaci

5. Sake duba mizanin albashin ma'aikatan majalisar tarayya

6. A daina dauko ma'aikatan majalisa marasa gogewa daga waje tunda na ciki sun fi su kwarewa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel