Zargin magudin jarabawa: An sake gurfanar da Sanata Adeleke a gaban kuliya

Zargin magudin jarabawa: An sake gurfanar da Sanata Adeleke a gaban kuliya

Tun a watan Satumban 2018 aka fara gurfanar da tsohon dan takarar gwamna a zaben gwamna na jihar Osun da aka gudanar a ranar 22 ga watan Satumba, Sanata Adeleke Ademola a gaban kotu da wasu mutane uku bisa zarginsu da hadin baki wajen tafka magudin zabe. Sai dai sun musanta aikata laifin amma a yanzu an sake gurfanar da su a gaban kotun.

A yau, Talata 18 ga watan Disamba ne gwamnatin tarayya ta sake gurfanar da Ademola Adeleke a gaban kotu bisa zarginsa da aikata laifuka bakwai masu alaka da magudin jarabawa.

Mr Adeleke ne dan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party, (PDP) a zaben gwamna da akayi a ranar 22 ga watan Satumbar 2018 a jihar Osun.

An dai fara gurfanar da Mr Adeleke ne a gaban mai shari'ah Edward Ekwo tare da wasu mutane hudu ne a watan Satumba inda ake tuhumarsu da aikata laifuka hudu.

Zargin magudin jarabawa: An sake gurfanar da dan takarar gwamna na PDP a kotu

Zargin magudin jarabawa: An sake gurfanar da dan takarar gwamna na PDP a kotu
Source: Twitter

Mr Adeleke da sauran wadanda akayi karar sun musanta zargin da ake musu bayan hakan ne lauya mai shigar da kara, Simon Lough ya bukaci kotu ta sanya ranar da za a cigaba da sauraron shari'ar.

Lauyan da ke kare wanda ake zargi, Alex Izinyon (SAN) ya roki kotu ta bashi lokaci domin ya amsa tambayoyin da kotu ta yiwa wanda ya ke karewa kuma a roki kotu bawa Sanata Adeleke damar fita kasar waje domin a duba lafiyarsa.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ta ruwaito cewa an gurfanar da Adeleke na a watan Satumba bisa zarginsa da aikata magudin zabe tare da wasu mutane uku da dan uwanda Sikiru Adeleke.

Sanatan ya musanta aikata laifin da ake zarginsa da shi kuma kotu ta bayar da belinsa saboda sanin da akayi masa.

Cikin ka'idojin belin, kotu ta bukaci Adeleke ya rika hallartar kotu duk lokacin da za a saurari shari'arsa kuma ya nemi izinin kotu kafin ya yi tafiya zuwa kasar waje.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel