2019: Dalilin da yasa ya zama dole a zabi PDP - Atiku

2019: Dalilin da yasa ya zama dole a zabi PDP - Atiku

- Dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar PDP ya ba yan Najeriya tabbacin zaman lafiya da ci gaba a fadin asar idan har aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a 2019

- Atiku ya bayar da tabbacin ne a gangamin da aka gudanar a yankin arewa maso gabas na jam’yyar a jihar Gombe a yau

- Ya bayyana cewa mutane na cikin yunwa da talauci, don haka akwai bukatar ayi waje da jam’iyyar All Progressives Congress (APC), domin samun karin ci gaba

Alhaji Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya ba yan Najeriya tabbacin zaman lafiya da ci gaba a fadin asar idan har aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a 2019.

Atiku ya bayar da tabbacin ne a gangamin da aka gudanar a yankin arewa maso gabas na jam’yyar a jihar Gombe a ranar Talata, 18 ga watan Disamba.

2019: Dalilin da yasa ya zama dole a zabi PDP - Atiku

2019: Dalilin da yasa ya zama dole a zabi PDP - Atiku
Source: Depositphotos

Ya bayyana cewa mutane na cikin yunwa da talauci, don haka akwai bukatar ayi waje da jam’iyyar All Progressives Congress (APC), domin samun karin ci gaba.

Atiku yayi kira ga magoya bayan jam’iyyar da su zabi PDP a dukkan matakai domin samun chanji mai kyau a kasar.

KU KARANTA KUMA: CUPP ta janye kiranta na a kauracewa gabatar da kasafin kudin 2019 da Buhari zai yi

A nashi bangaren,gwamnan jihar Gombe Ibrahim Dankwambo, wanda ya kasance jagoran gangamin shugaban kasa a yankin arewa maso gabas ya gode ma shugabancin jam’iyyar da ta ba yankin tikitin takarar shugaban kasar.

Yayi kira ga mutanen yankin arewa maso gabas da dawo da martabarsu ta hanyar tabbatar da nasarar jam’iyyar a 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel