CUPP ta janye kiranta na a kauracewa gabatar da kasafin kudin 2019 da Buhari zai yi

CUPP ta janye kiranta na a kauracewa gabatar da kasafin kudin 2019 da Buhari zai yi

- Jam’iyyar hadin gwiwa ta CUPP ta janye kira da tayi wa yan majalisun dokokin kasar na su kauracewa ma zaman ranar Laraba

- A zaman ne dai ake sanya ran shugaban kasa Muhammadu Buhari zai gabatar da kasafin kudin 2019

- CUPP tace tacanja matsayarta akan lamarin biyo bayan sanya baki da shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara suka yi

Gamayyar kungiyar Coalition of United Political Parties (CUPP) a ranar Talata, 18 ga watan Disamba ta janye kira da tayi way an majalisun dokokin kasar na su kauracewa ma zaman ranar Laraba inda anan ne shugaban kasa Muhammadu Buhari zai gabatar da kasafin kudin 2019.

Yanzu Yanzu: CUPP ta janye kiranta na a kauracewa gabatar da kasafin kudin 2019 da Buhari zai yi

Yanzu Yanzu: CUPP ta janye kiranta na a kauracewa gabatar da kasafin kudin 2019 da Buhari zai yi
Source: Depositphotos

Kakakin kungiyar na farko, Imo Ugochinyere a wani jawabi da yayi ga manema labarai yace CUPP ta canja matsayarta ak lamarin biyo bayan sanya baki da shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara suka yi tare da wasu tsoffin shugabannin kasa biyu da ba’a fadi sunayensu ba.

Ugochinyere ya kuma yi kira ga yan majalis da su dubi takardun da kyau idan aka gabatar da shi.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya koka da ayyukan Kungiyar Amnesty International

Duk da janye batun kauracewar, yace CUPP na nan akan bakarta na farko cewa gwamnati mai ci na fakewa da kariyarta.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel