Korar Mourinho: Darajar hannun jarin kungiyar Manchester United ya tashi a kasuwa

Korar Mourinho: Darajar hannun jarin kungiyar Manchester United ya tashi a kasuwa

Darajar hannun jarin kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ya tashi a kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Frankfurt dake kasar Jamus bayan kungiyar ta sallami kociyanta, Jose Mourinho, a yau, Talata.

Hakan ya nuna cewar masu sayen hannayen jari sun ji dadi da shawarar da mahukuntan kungiyar Manchester United suka yi na sallamar Mourinho.

Manchester united ta yanke shawarar sallamar Mourinho ne bayan abokiyar hamayyarta, kungiyar Liverpool, ta doke ta da ci 3 da 1 a wasan gasar cin kofin Firemiya na kasar Ingila da suka buga ranar Lahadi da ta gabata.

Korar Mourinho: Darajar hannun jarin kungiyar Manchester United ya tashi a kasuwa

Mourinho
Source: Getty Images

Rashin samun nasara a wasan ya bar kungiyar Manchester United a mataki na 6 a kan teburin gasar Firemiya da banbancin maki 19 tsakaninsu da kungiyar Liverpool dake mataki na 1.

DUBA WANNAN: Kyan tafiya: Ronaldo zai koma Madrid

Wannnan shine karo na farko tun shekarar 2002 da Mourinho ya taba barin wata kungiya ba tare da lashe kofi ko daya ba.

Kafin sallamar sa a yau, Mourinho ya shafe shekaru biyu yana horar da kungiyar Manchester United.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel