Ana wata ga wata: Jami'ar ABU ta bi sahun SSANU na shiga yajin aiki

Ana wata ga wata: Jami'ar ABU ta bi sahun SSANU na shiga yajin aiki

Rahotannin da Legit.ng Hausa ke samu yanzu na nuni da cewa kungiyar manyan malaman jami'o'i na kasa reshen jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, ta shiga yajin aikin gargadi na kwanaki 3 wanda uwar kungiyar ta kasa ta shiga.

Shugaban kungiyar manyan malaman jami'o'i ta kasa SSANU reshen jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, Shuaibu Halili, ya bayyana cewa kungiyar ta bi sahun uwar kungiyar ta kasa wajen shiga yajin aikin gargadi na kwanaki uku.

Shuaibu Halili, ya sanar da hakan ne a ranar Talata, lokacin wata zanga zangar lumana da aka gudanar a sashen jami'ar na din-din na jami'ar ta ABU.

KARANTA WANNAN: KARIN BAYANI: Babu sauran sasanci tsakanin ASUU, ASUP da gwamnatin tarayya har sai Janairu

Ana wata ga wata: Jami'ar ABU ta bi sahun SSANU na shiga yajin aiki

Ana wata ga wata: Jami'ar ABU ta bi sahun SSANU na shiga yajin aiki
Source: Depositphotos

Halili ya ce reshen kungiyar na jami'ar ya yanke hukuncin shiga yajin aikin ne sakamaon gazawar gwamnatin tarayya na bin wani umurni da kotu ta bayar na mayar da malaman da ke koyarwa a kananan makarantun da ke cikin jami'o'i da aka sallama, a bakin aikinsu.

Wasu dalilan da suka tilasta kungiyar shiga yajin aikin, a cewarsa, sun hada da rashin biyan N8bn da alawus a manyan malaman, 'yan watanni kadan bayan da gwamnatin tarayya ta biya ASUU Naira biliyan 23.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel