KARIN BAYANI: Babu sauran sasanci tsakanin ASUU, ASUP da gwamnatin tarayya har sai Janairu

KARIN BAYANI: Babu sauran sasanci tsakanin ASUU, ASUP da gwamnatin tarayya har sai Janairu

- Zaman sulhun da ya gudana tsakanin kungiyar ASUU da gwamnatin tarayya ya kare ba tare da an cimma wata matsaya na kawo karshen yajin aikin da kungiyar ta shiga ba

- Har yanzu dai kungiyar ASUU na fafutukar ganin cewa gwamnati ta biya kudaden da aka kulla yarjejeniyar basu tun a shekarar 2009

- Sai dai ministan kwadago da daukar ma'aikata, Chris Ngige, ya baiwa dalibai hakuri, da basu tabbacin cewa a ciki wata Janairu gwamnati zata kawo karshen yajin aikin

Zaman sulhun da ya gudana tsakanin kungiyar malaman jami'o'i na kasa ASUU da gwamnatin tarayya ya kare ba tare da an cimma wata matsaya kan yajin aikin da kungiyar malaman ta shiga ba, haka kuma an dage zaman har sai baba ta gani.

Farfesa Biodun Ogunyemi, shugaban ASUU na kasa wanda ya ki cewa uffan ga manema labarai jim kadan bayan fitowarsu daga zaman da suka yi da gwamnatin da suka shafe sama da awanni biyu suna yi a ranar Litinin, ya ce "Ku je ku tambayi ministan Kwagado da daukar ma'aikata, Sanata Chris Ngige kan sakamakon ganawar."

Har yanzu dai kungiyar ASUU na fafutukar ganin cewa gwamnati ta biya kudaden da aka kulla yarjejeniyar basu tun a shekarar 2009, da kuma sabuwar jarjejeniyarsu da gwamnati a 2017, wanda gaza cika wannan alkawarin ne ya sa kungiyar shiga yajin aikin sai baba ta gani.

KARANTA WANNAN: Zargin satar jarabawa: Rundunar 'yan sanda ta gurfanar da Adeleke a gaban kotu

KARIN BAYANI: Babu sauran sasanci tsakanin ASUU, ASUP da gwamnatin tarayya har sai Janairu

KARIN BAYANI: Babu sauran sasanci tsakanin ASUU, ASUP da gwamnatin tarayya har sai Janairu
Source: Depositphotos

Sai dai Chris Ngige, a zantawarsa da manema labarai, ya ce taron dai ci gaba ne ga wanda aka fara a ranar Litinin din makon da ya gabata, sai dai ba a cimma matsaya ba, duk da cewa an raba aiki tsakanin ma'aikatu, hukumomi, da kuma sassa na gwamnati do gano mafita kan lamarin.

Ministan ya kuma karyata cewa kungiyar ta fice daga dakin tattaunawa yana mai cewa ba haka lamarin ya faru ba, "mun gudanar da zaman ne cikin fahimtar juna, daga baya ma har muka tattauna akan wasu fannonin daban."

"Don haka muke baiwa dalibai da ke zaune a gida hakuri, muna sa ran kawo karshen yajin aikin a watan Janairu, ga wadanda ke zana jarabawa, muna fatan kawo maslaha don su kammala a satin farko na watan Janairu," a cewar ministan.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel