Ba zamu hana Buhari gabatar da kasafin kudin 2019 ba - Ma'aikatan Majalisa

Ba zamu hana Buhari gabatar da kasafin kudin 2019 ba - Ma'aikatan Majalisa

Bature Mohammed, shugaban ma'aikatan majalisar tarayya (PASAN) ya ce mai'aikatan majalisar tarayya da ke zanga-zanga sun ce ba za su hana shugaba Muhammadu Buhari shiga harabar majalisar ba domin gabatar da kasafin kudin shekarar 2019 ga 'yan majalisar ba.

A yayin da ya ke magana a lokacin da jami'an 'yan sanda suka mamaye harabar majalisar a ranar Talata, Mr Mohammed ya ce shugaban kasa yana iya zuwa majalisar ya gabatar da kasafin kudin a duk lokacin da ya shirya.

Shugaba Buhari zai tafi majalisar domin gabatar da kasafin kudin ne a ranar Laraba. Sai dai ana tunanin yajin aikin gargadi na kwanaki hudu da ma'aikatan majalisar suka fara a ranar Litinin na iya shafansa.

DUBA WANNAN: Barazana ga demokradiyya: Ku sa ido a kan Shehu Sani, Danjuma ya gargadi hukumomin tsaro

Ma'aikatan majalisar sun garkame kofar shiga majalisar a ranar Litinin wadda hakan ya janyo cinkoson motocci da mutane.

Ba zamu hana Buhari gabatar da kasafin kudin 2019 ba - Ma'aikatan Majalisa

Ba zamu hana Buhari gabatar da kasafin kudin 2019 ba - Ma'aikatan Majalisa
Source: Twitter

A bangarensu, shugabanin majalisar sun bukaci jami'an 'yan sanda da SSS su tsare harabar majalisar domin zaman da za a yi a ranar Talata.

'Yan majalisar sun saba zamansu ne a ranakun Talata, Laraba da Alhamis na kowanne mako.

Domin cika wannan umurni, jami'an 'yan sanda sun mamaye harabar majalisar a ranar Talata inda suka hana ma'aikata da 'yan jarida daga shiga harabar majalisar.

Daga bisani dai an bari wasu 'yan jarida sun shiga harabar majalisar.

Mr Mohammed ya ce 'yan majalisar sun munana lamarin ne a lokacin da suka bawa 'yan sanda umurnin mamaye majalisar.

"Shugabanin majalisa sun kara munana lamarin ne a lokacin da suka umurci 'yan sanda su hana ma'aikatan mu shiga majalisar."

Sai dai duk da hakan shugaban kasa yana iya zuwa ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2019 a duk lokacin da ya shirya.

"Ba mu da niyyar hana shugaban kasa gabatar da kasafin kudi. Idan har zamu bari masu shara da masu aikin banki su gudanar da ayyukansu, ta yaya za mu hana shugaban kasa gabatar da kasafin kudi? Amma matakin da shugabanin majalisa suka dauka na kulle majalisar ba dai-dai bane. Ba mune muka kulle kofar majalisar ba

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel