Shugaba Buhari ya koka da ayyukan Kungiyar Amnesty International

Shugaba Buhari ya koka da ayyukan Kungiyar Amnesty International

- Shugaba Buhari ya nuna rashin jin dadi kan yadda Kungiyar Amnesty International ke nuna bangarancia rahotannin da ta ke fitarwa akan yaki da yan ta’addan Boko Haram

- Garba Shehu, ya bayyana damuwar gwamnati a kan irin rahotannin son zuciya da gwamnati ke zargin Amnesty International da fitarwa

- Buhari ya roki kungiyar da ta yi duba da binciken ayyukan jami’an ta a Najeriya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya koka da yadda Kungiyar Amnesty International ke nuna bangaranci da kuma rashin adalci a rahotannin da ta ke fitarwa game da kasar Najeriya da kuma yaki da yan ta’addan Boko Haram.

A makon da ya gabata ne sojojin kasar suka bayar da sanarwar korar kungiyar daga ayyukan jinkai da ta ke yi a yankin da ake yaki da Boko Haram.

Sai dai kuma kwana daya bayan korar, aka janye batun inda fadar shugaban kasa ta fito ta ce bangarorin biyu za su yi zaman sasanci domin gano inda matsalar ta ke.

Shugaba Buhari ya koka da ayyukan Kungiyar Amnesty International

Shugaba Buhari ya koka da ayyukan Kungiyar Amnesty International
Source: Depositphotos

Kwana biyu bayan nan kuma sai sojoji suka kara jaddada cewa lallai ba su bukatar Amnesty International a yankin Arewa maso gabashin kasar.

Jiya Litinin, 17 ga watan Disamba kuma, sai mai Magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya bayyana damuwar gwamnati a kan irin rahotannin son zuciya da gwamnati ke zargin Amnesty International da fitarwa.

Sanarwar da Garba ya fitar daga fadar Shugaban Kasa ta nuna cewa duk da gwamnatin Buhari ta yarda kuma ta na bada hadin kai kan dalilan kafa kungiyar Amnesty, amma gwamnatin ta hakkake cewa kungiyar na kawo mata cikar wajen yaki da Boko Haram, musamman wajen karya guyawun sojojin Najeriya daga irin rahotannin da ta ke fitarwa.

KU KARANTA KUMA: Kaso 90 na yan Najeriya sun yanke shawarar zabar Atiku - Fayose

Buhari ya ce gwamnati na ganin kamar ma ta na yaki biyu ne a lokaci guda. Na farko yaki da Boko Haram, na biyu kuma yaki da Amnesty International.

Daga karshe ya roki kungiyar da ta yi duba da binciken ayyukan jami’an ta a Najeriya, musammaan a kan batun da ya shafi yaki da ta’addanci.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel