Zargin satar jarabawa: Rundunar 'yan sanda ta gurfanar da Adeleke a gaban kotu

Zargin satar jarabawa: Rundunar 'yan sanda ta gurfanar da Adeleke a gaban kotu

- Rundunar 'yan sanda ta sake gurfanar da dan takarar gwamnan jihar Osun karkashin jam'iyyar PDP, Ademola Adeleke gaban kotu, kan zarginsa da satar jarabawar WAEC

- A karon farko rundunar ta gurfanar da Adeleke ne kan zargin aikata laifuka 4, sai dai a ranar Takalata, ta sake gurfanar da shi akan aikata laifuka 7

- Rundunar 'yan sanda na zargin Adeleke da hada baki da ma'aikatan wata makaranta, wajen samun sakamakon jarabawar na bogi, da buga bayanan haihuwarsa na karya

A ranar Talata, rundunar 'yan sanda ta sake gurfanar da dan takarar gwamnan jihar Osun karkashin jam'iyyar PDP, Ademola Adeleke gaban kotu, kan zarginsa da satar jarabawar WAEC.

Mr. Adeleke wanda aka fara gurfanar da shi kan zarginsa da aikata laifuka hudu wanda aka gabatarwa kotun a cikin watan Satumba, an kuma sake gurfanar da shi a ranar Talatar, inda aka kara tuhumarsa da laifuka bakwai, duka akan zargin satar jarabawar.

Rundunar 'yan sanda na zargin Adeleke da hada baki da ma'aikatan makarantar Ojo-Aro community grammar, wajen samun sakamakon jarabawar na bogi, kuma hakan ne ma yasa rundunar 'yan sandata gurfanar a Adeleke tare da shugaban makarantar da wasu ma'aikata uku da ake zarginsu da aikata laifin tare.

KARANTA WANNAN: 2018: Mun saka jarin $100m a Nigeria - Gwamnatin kasar Sin

Zargin satar jarabawa: Rundunar 'yan sanda ta gurfanar da Adeleke a gaban kotu

Zargin satar jarabawa: Rundunar 'yan sanda ta gurfanar da Adeleke a gaban kotu
Source: UGC

Rundunar 'yan sanda ta kuma zargi Mr Adeleke da buga takardun bogi, akan batun da ya shafi gaskiya kan yawan shekarunsa da kuma karya dokar satar amsar jarabawa ta CAP E15, 2004.

Mr. Adeleke, wanda ya kusan yin kunnen doki da abokin karawarsa najam'iyyar APC, Adegboyega Oyetola, na ci gaba da kalubalantar sakamakon zaben wanda ya bayyana Mr Oyetola a matsayin wanda ya lashe zaben.

Mr Adeleke dai na zargin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da kuma jam'iyyar ACP na hada hannu wajen ganin cewa dan takarar APC ne ya lashe zaben da aka gudanar a watan Satumbar wannan shekarar.

Dan takarar jam'iyyar PDP da kuma jam'iyyarsa na zargin rundunar 'yansa da hada kai da jam'iyyar APC na gallazawa Mr Adeleke.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel