Sama da yan Kwankwasiyya 25,000 sun koma APC a jihar Kano

Sama da yan Kwankwasiyya 25,000 sun koma APC a jihar Kano

- Jam'iyyar APC a jihar Kano ta samu karuwa yayinda yan Kwankwasiyya 25,000 suka koma jam'iyyar

- Gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi lale marhabun ga wadannan jama'a

- Ganduje, ya tabbatar musu da cewa ba zasu zama saniyar ware ba a jam'iyyar Adamawa

Sama da mambobin kungiyar siyasar Kwankwasiyya daga mazabar Kano ta kudu sun sauya sheka daga jam'iyyar Peoples Democratic Party zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya tarbi masu sauya shekan a taron yakin neman zaben yankin Kano ta kudu inda ya mika tutar jam'iyyar APC ga yan takaran kujeran majaisar wakilai da na dokokin jihar a zaben 2019.

KU KARANTA: Hisbah ta damke mata 11 a bikin daurin auren yan madugo a jihar Kano

Masu sauya shekan sun halarci taron kaddamar da yakin neman zaben Sanata Kabiru Gaya a karamar hukumar Rano dake jihar Kano.

A taron, gwamna Ganduje ya bayyana cewa irin nasarorin da jam'iyyar APC ta samu a tarayya da jihohi, ya isa jam'iyyar ta samu nasara a shekarar 2019.

Gwamnan yace: "Irin namijin aikin da shugaba Muhammadu Buhari keyi na kawo cigaban kasa a kowani fanni, musamman a wuraren tsaro, tattalin arziki da samar da aikinyi, na kara mana karfin gwiwa domin 2019."

Ya tabbatarwa masu sauya sheka cewa ba za'a zamar da su saniyar ware a jam'iyyar ba. Ya basu tabbacin cewa lokaci ya zo da jama'a zasu amfana da romon demokradiyya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel