Ko Buhari zai iya zuwa Muhawarar? Jami'ar Cambridge tace zata yi wa 'yan takarar 2019 lale

Ko Buhari zai iya zuwa Muhawarar? Jami'ar Cambridge tace zata yi wa 'yan takarar 2019 lale

- Jami'ar Cambridge zasu tattauna da yan takarar shugabancin kasa

- Za'a gudanar da taron a watan Junairu shekara ta 2019

- Zai bawa shuwagabannin damar bayyanawa yan kasar kudirorin su

Ko Buhari zai iya zuwa Muhawarar? Jami'ar Cambridge tace zata yi wa 'yan takarar 2019 lale

Ko Buhari zai iya zuwa Muhawarar? Jami'ar Cambridge tace zata yi wa 'yan takarar 2019 lale
Source: Twitter

Jami'ar Cambridge (CUACS) da kuma kungiyar Cambridge sun hadawa yan takarar shugabancin kasa su Biyar wani taro akan zaben shekara ta 2019.

Taron mai taken "2019 presidential Election Forum" zai gudana a watan Yanairu shekara ta 2019.

Taron wanda jagoran shirin Semilore Delano ya sanya hannu ya bayyana a ranar 13 ga watan Disemba cewa "Shirin zai bawa shuwagabannin damar bayyanawa yan Najeriya kudirrikan su".

Zaben wanda zai gudana a 16 ga watan Fabrairu shekara ta 2019 wanda wannan tattaunawa itace dama ta karshe da yan takarar suke da ita na bayyana kudirin su.

DUBA WANNAN: Tsage gaskiya: Aikin waye kawo jirgin kasa daga Abuja zuwa jihohi?

Martine Dennis kwararriyar yar jaridar nan ta Aljazeera zata samu halartar taron.

Tana da kwarewar shekaru 35 a fannin aikin jarida wanda ya hada da aiki a BBC.

Wannan taro na yan takarar shugabancin kasa su Biyar ya hada da Shugaban kasa Muhammad Buhari,Atiku Abubakar, Donald Duke, Kingsley Chiedu da kuma Oby Ezekwesili.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa.

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel