Alkali ya bada belin Shugaban Hukumar NBA, Paul Usoro a kan Miliyan 250

Alkali ya bada belin Shugaban Hukumar NBA, Paul Usoro a kan Miliyan 250

Dazu nan mu ka ji cewa Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Kasa zagon kasa ta maka Shugaban Lauyoyin Najeriya, Paul Usoro, a gaban babban Kotun Tarayya da ke cikin Garin Legas.

Alkali ya bada belin Shugaban Hukumar NBA, Paul Usoro a kan Miliyan 250

An daga shari’ar Usoro sai zuwa farkon Watan Fubrairu
Source: Depositphotos

Paul Usoro da wasu manya a Gwamnatin Jihar Akwa-Ibom su na gaban Alkalin babban Kotun Tarayya na Legas yanzu haka, inda su ke amsa tambayoyi game da zargin awon gaba da wasu kudi da su ka haura Naira Biliyan 1.4.

Usoro wanda shi ne Shugaban Kungiyar NBA ya fadawa Alkali Muslim Hassan cewa bai aikata laifin da ake zargin sa da su ba. Sauran wadanda ake tuhuma da laifi sun hada Kwamishinan kudi na Jihar Akwa-Ibom, Nsikan Nkan.

KU KARANTA: Hukumar EFCC ta gurfanar da wani matashi mai yi wa kasa hidima

Haka kuma Kotun da ke zama a Jihar Legas tana zargin babban Akanta Jihar Akwa Ibom watau Mfon Udomah; da wata Baiwar Allah mai suna Margaret Ukpe da kuma Kwamishinan shari’a na Jihar watau Uwemedimo Nwoko.

Babban Lauya Rotimi Oyedepo shi ne ya tsayawa EFCC yayin da Cif Wole Olanipekun (SAN) da wasu manyan Lauyoyi su ka tsaya domin kare Shugaban Lauyoyin na Najeriya watau Paul Usoro wanda ake tuhuma da laifuffuka 10.

KU KARANTA: Gwamnatin kasar Sin ta zuba jarin Dala Miliyan $100m a Najeriya a bana

Wole Olanipekun wanda yake kare wanda ake zargi, yana neman Kotu ta dauke shari’ar daga Legas zuwa Birnin Uyo a cikin Jihar Akwa Ibom ko kuma Garin Abuja. Olanipekun ya nemi Kotu ta dakata kafin ta gurfanar da Usoro.

Shi dai wanda ake tuhuma ya nemi Alkali ya bada belin sa a matsayin sa na sanannen mutum kuma Shugaban Kungiyar NBA ta kasa. Alkali Muslim ya dage karar ya kuma bada belin Lauyan a kan kudi Naira miliyan 250 tare da jingina.

Alkali mai shari'a Muslim Hassan ya dage karar har sai zuwa 5 ga Watan Fabrairu da kuma 5 ga Watan Maris na 2019 kamar yadda mu ka samu labari daga Hukumar NAN bayan zaman da aka yi a yau dinnan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel