Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya tafi kasar Nijar

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya tafi kasar Nijar

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya tafi jamhurriyar Nijar a ranan Talata, 18 ga watan Disamba 2018 domin halartan taron murnan ranan tunawa da kafa Nijar kafin ta samu yancin kai a shekarar 1960.

Game da cewar mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, Gwamnatin kasar Nijar ce ta gayyaci shugaba Muhammadu a matsayin bako na musamman a wannan muhimmin taro.

Mai magana da yawun shugaban kasan, ya saki wannan jawabi ne a rana Litinin cewa Buhari zai yi tafiyar kwana daya domin halartan taron bikin murnan shekara 60 da samun jamhuriyyar Nijar.

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya tafi kasar Nijar

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya tafi kasar Nijar
Source: Twitter

KU KARANTA: Jihar Legas zata baiwa Buhari kuri'u milyan 3 a 2019 - Tinubu

Yace: "A gayyatan da shugaban kasan Nijar Mahamadou Issoufou, ya aikowa shugaba Buhari, zai zama bako na musamman a matsayinsa na makwabcin kasar Nijar."

"Wannan taron da shugaba Buhari zai halarta zai kara zurfafa alaka da zumunci tsakanin gwamnatocin biyu da yan kasashensu."

Wadanda zasu raka Buhari sune gwamnan jihar Jigawa, Mohammed Badaru Abubakar; gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i; da gwamnan jihar Osun, Adegboyega Oyetola Isiaka na jihar Osun."

Sauran sune dogarinsa da karamar ministar harkokin wajen Najeriya, Khadija Bukar Abba Ibrahim.”

Shugaba Buhari zai tafi ne bayan bikin murnar cikansa shekaru 76 a duniya da akayi a fadar shugaban kasa yau.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel