Jinkirin nada ministoci: Jonathan ya yiwa Buhari raddi

Jinkirin nada ministoci: Jonathan ya yiwa Buhari raddi

- Tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan ya bukaci shugaba Buhari ya fuskanci matsalar da ke gabansa

- Goodluck Jonathan ya ce gwamnatinsa ba ta da hannu cikin jinkirin da gwamnatin Buhari tayi kafin nada ministoci

- Jonathan ya ce abin mamaki ne bayan shekaru uku a kan mulki har yanzu gwamnatin shugaba Buhari tana neman wanda za ta jingina wa laifi

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ce gwamnatinsa ba ta da hannu cikin matsalolin da gwamnatin Buhari ke ciki kuma ya bukaci shugaba Muhammadu Buhari ya nemi wani daban da zai dora wa laifi ba shi ba.

Jinkirin nada ministoci: Jonathan ya yiwa Buhari raddi

Jinkirin nada ministoci: Jonathan ya yiwa Buhari raddi
Source: Facebook

Tsohon shugaban kasar yana mayar da martani ne a kan kalaman babban mai taimakawa shugaban kasa na musamman a kan kafofin watsa labarai, Garba Shehu ya furta inda ya ce laifin Jonathan ne Buhari ya yi jinkirin nada ministocinsa yayin da ya karbi mulki.

DUBA WANNAN: Barazana ga demokradiyya: Ku sa ido a kan Shehu Sani, Danjuma ya gargadi hukumomin tsaro

Shugaban kasar da aka rantsar a ranar 29 ga watan Mayun 2015 bai nada ministocinsa ba sai bayan wattani shida wadda hakan ya janyo cece-kuce a kasar a wannan lokacin.

A hirar da akayi dashi a Channels Television, Garba Shehu ya yi ikirarin cewa tsohon shugaban kasa Jonathan ne ya janyo jinkirin saboda rashin bayar da hadin kai ga kwamitin sauya mulki.

Sai dai a wata sanarwa da ya fitar ta bakin mai magana da yawunsa, Ikechukwu Eze, Mr Jonathan ya ce abin mamaki ne yada bayan shekaru uku shugaban kasar yana neman wadanda zai jinginawa laifi.

"Wannan lamarin karara ya ke, gwamnatin Jonathan ba ta da hannu cikin jinkirin da gwamnatinsa tayi kafin nada ministoci da za su janyo hankalin masu saka hannun jari a kasar saboda takardun sauya mulki ba shi da wani alaka da ministoci."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel