Zargin Damfara: Hukumar EFCC ta gurfanar da matashi dan bautar kasa

Zargin Damfara: Hukumar EFCC ta gurfanar da matashi dan bautar kasa

Hukumar yaki masu yiwa arzikin kasa ta'annati EFCC ta gurfanar da wani wani mai yiwa kasa hidima, Ogbonna Victor Chibuzor a gaban mai shari'a Mohammed Liman na Kotun tarayya da ke Enugu bisa zarginsa da aikata damfara.

Sanarwar da ta fito daga bakin mai magana da yawun EFCC, Mr Chris Oluka ta ce ana zargin Ogbonna ne da aikata laifuka 5 wanda suka hada da damfara da mallakar takardun bogi wanda hakan ya sashi na 6 na dokar damfarar kudade na 2006.

Ya ce an kama Ogbonna ne sakamakon wata sumame da hukumar tayi a makon da ya gabata inda suka kama wasu matasa da dama wadanda aka lura suna rayuwa cikin daula duk da cewa babu wanda ya san sana'ar da suke yi.

Zargin Damfara: Hukumar EFCC ta gurfanar da matashi dan bautar kasa

Zargin Damfara: Hukumar EFCC ta gurfanar da matashi dan bautar kasa
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Barazana ga demokradiyya: Ku sa ido a kan Shehu Sani, Danjuma ya gargadi hukumomin tsaro

"Binciken da aka gudanar a cikin kwamfutan dan damfarar da ake zargi ya bayyana wasu takardu da ya mallaka domin amfani da su wajen damfarar 'yan Najeriya da 'yan kasashen waje ma," inji Oluka.

Ya kara da cewa an kuma samu wasu sakonnin email da ke nunan Ogbanna ya yunkurin damfara wasu 'yan kasashen waje a Amurka da Ingila inda ya ke tambaya a turo masa wasu kudade.

A cewar Oluka, wanda ake zargin ya ce shi bai aikata laifi ba wadda hakan ya sa lauya mai kare wanda ake zargi, E.O. Isiwu ya bukaci a bayar da shi beli amma lauyan da ya shigar da kara Innocent Mbachie ya ki amincewa da hakan.

Sai dai duk da hakan, Alkalin kotun, ya bayar da belin wanda ake zargin a kan kudi N500,000 da bukatar a gabatar da mutum guda wanda zai karbi belin.

Ya bayar da umurnin a cigaba da rike Ogbonna a gidan yari har zuwa lokacin da aka cika ka'idojin belinsa sannan ya daga cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 30 ga watan Janairun 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel