Jihar Legas zata baiwa Buhari kuri'u milyan 3 a 2019 - Tinubu

Jihar Legas zata baiwa Buhari kuri'u milyan 3 a 2019 - Tinubu

Babban jigon jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Tinubu, ya yi kira ga dukkan mambobin jam'iyyar a jihar Legas sun fara yakin neman zabe domin tabbatar da cewa an baiwa jam'iyyar kuri'u miliyan uku a zaben bana.

Tinubu, wanda tsohon gwamna ne a jihar Legas ya bayyana hakan ne a taron masu ruwa da tsakin jam'iyyar da aka gudanar a sakatariyansu dake Ikeja, Legas.

Game da cewar Tinubu, jihar Legas na da kuri'u miliyan shida kuma ya zama wajibi jam'iyyar ta nemi akalla rabin wadannan kuri'u.

Ya kara da cewa kada su damu da irin noke-noke da kaidin da jam'iyyar adawa ta PDP ke shiryawa a jihar.

Jihar Legas zata baiwa Buhari kuri'u milyan 3 a 2019 - Tinubu

Jihar Legas zata baiwa Buhari kuri'u milyan 3 a 2019 - Tinubu
Source: UGC

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Kungiyar kwallon Manchester United ta sallami Jose Mourinho

Yace: "Sama da shekaru 16 kenan da suke alkawura basu cikawa. Mu a jihar Legas, mun kasance a jam'iyyar adawa a sama, kuma sun tsira, mun cigaba. Mune na biyar a girman tattalin arziki a nahiyar Afrika. Legas na da kuri'u milyan shida."

"Na kalubalanceku duka; wajibi ne ku kawo kashi 50 cikin 100 kuri'unku ga APC; akalla kashi 50 cikin 100 na mutane miliyan shida."

A bangare guda, gwamnan jihar Legas, Akinwumi Ambode, ya bukaci dukkan wadanda suke ganin an zaluncesa suyi hauri kamar yadda yayi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel