Zanga-zangan ma’aikatan majalisa: Laifin Saraki da Dogara ne - APC

Zanga-zangan ma’aikatan majalisa: Laifin Saraki da Dogara ne - APC

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta ga laifin shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, kan zanga-zangan da ma’aikatan majalisar dokokin kasar suka gudanar kuma suke kan gudanarwa.

Ma’aikatan sun fara yajin aikin kwanaki hudu a ranar Litinin, 17 ga watan Disamba inda suka bukaci a biyasu alawus dinsu sannan kara ma wadanda suka isa Karin girma a cikinsu.

A ranar Litinin, sun hana yan majalisa da sauran mutane shiga harabar majalisar dokokin.

Zanga-zangan ma’aikatan majalisa: Laifin Saraki da Dogara ne - APC

Zanga-zangan ma’aikatan majalisa: Laifin Saraki da Dogara ne - APC
Source: Original

Magatakardan majalisar dokoki, Sanni Omolori, ya daura laifin akan rashin sakin kuadade da gwamnatin tarayya bata yi ba a matsayin dalilin rashin biyan ma’aikatan hakkinsu.

A wata sanarwa daga kakakinta, Lanre Issa-Onilu a ranar Talata, 18 ga watan Disamba APC tayi watsi da zargin cewa gwamnatin ta ce bata saki kudade ba, amma maimakon haka sai tad aura laifin kan shugabannin majalisar dokokin wadanda suka sauya sheka zuwa babbar jam’iyyar adawa wato PDP.

Mista Issa-Onilu ya bayyana zanga-zangan a matsayin abun kunya da kuma wani tuni ga abunda yace yan Najeriya sun fuskanta a karkashin gwamnatin Peoples Democratic Party (PDP).

KU KARANTA KUMA: Ma’aikata sun yanke wuta da hanyar ruwa na majalisar dokokin kasar

Yace idan da’ace shugabannin majalisar dokokin sun mayar da hankalinsu akan aikin da ya rataya a wuyansu maimakon tsoma baki a lamarin da bai shafe su bad a kokarin tozarta gwamnatin APC , da basu wofantar da jin dadin ma’aikatansu ba.

Jam’iyyar tace jin dadin ma’aikata shine manfar gwamnatin APC sannan tayi kira ga shugabannin majalisar dokoki karkashin mambobin PDP da su ceto kasar daga wannan abun kunyan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel