Yanzu Yanzu: Yan sanda sun mamaye majalisar dokokin kasar, sunyiwa mashigin kawanya

Yanzu Yanzu: Yan sanda sun mamaye majalisar dokokin kasar, sunyiwa mashigin kawanya

- Jami’an yan sandan Najeriya sun mamaye majalisar dokokin kasar

- Yan sandan sun kuma rufe dukkanin mashigin harabar majalisar sun hana ma’aikata samun damar shiga ciki

- Hakan ya biyo bayan umurnin da shugabannin majalisar suka ba hukumomin tsaro cewa su tsare harabar majalisar gabannin kaddamar da kasafin kudin 2019 wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi a ranar Laraba

Jami’an rundunar yan sandan Najeriya sun mamaye majalisar dokokin kasar. Jami’an wanda suka rufe dukkanin mashigin harabar majalisar sun hana ma’aikata samun damar shiga ciki.

An kewaye babban mashigin majalisar da ke kusa da Eagle Square da motocin sintiri.

Jami’an tsaron sun kyale yan jarida, ma’aikatan gini, masu siyar da jarida da wasu yan tsiraru da suke ganin ya kamara a bari su shiga.

Yanzu Yanzu: Yan sanda sun mamaye majalisar dokokin kasar, sunyiwa mashigin kawanya

Yanzu Yanzu: Yan sanda sun mamaye majalisar dokokin kasar, sunyiwa mashigin kawanya
Source: Depositphotos

Ma’aikatan karkashin kungiyar Parliamentary Staff Association of Nigeria (PASAN) sun tsayar da abubuwa a harabar majalisar duk a cikin yajin aikin kwanaki hudu da suka tafi.

KU KARANTA KUMA: Kaso 90 na yan Najeriya sun yanke shawarar zabar Atiku - Fayose

A safiyar ranar Litinin, 17 ga watan Disamba sun mamaye mashigin majalisar sannan suka tsige wuta da hanyar da ake samun ruwa zuwa cikin ginin majalisar.

Shugabanni da hukumar majalisar dokokin sun yi wani ganawar gaggawa a daren jiya inda suka umurci yan sanda da na yan sandan farin kaya da su tsare harabar majalisar gabannin kaddamar da kasafin kudin 2019 wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi a ranar Laraba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel