Ma’aikata sun yanke wuta da hanyar ruwa na majalisar dokokin kasar

Ma’aikata sun yanke wuta da hanyar ruwa na majalisar dokokin kasar

- Ma’aikatan majalisar dokokin sun yi zanga-zanga inda suka yanke wuta da hanyar ruwan famfo a majalisar dokokin kasar domin fara yajin aikin jan kunne na kwanaki hudu

- Sun yi wa mashigin majalisar kawanya domin ci gaba da neman hakkinsu na biyansu albashin da suke bi da alawus da kuma sauran kudadensu

- Rashin wutar lantarki da wuta a majalisar ya tursasa yan majalisar da sauran ma’aikatan da suka sam damar shiga ofishinsu gaggawar barin majalisar

Ma’aikatan majalisar dokokin kasar karkashin kungiyar Parliamentary Staff Association of Nigeria (PASAN), a jiya sun yi zanga-zanga inda suka yanke wuta da hanyar ruwan famfo a majalisar dokokin kasar domin fara yajin aikin jan kunne na kwanaki hudu.

Ma’aikatan wadanda suka mamaye majalisar dokokin da misalin 6:30 na safe, sunyi wa dukkanin mashigin majalisar kawanya domin ci gaba da neman hakkinsu na biyansu albashin da suke bi da alawus da kuma sauran kudadensu.

Ma’aikata sun yanke wuta da hanyar ruwana majalisar dokokin kasar

Ma’aikata sun yanke wuta da hanyar ruwana majalisar dokokin kasar
Source: Depositphotos

Ma’aikatan majalisan na son ayi masu Karin albashi da kaso 28 karkashin amincewar CONLESS 2010.

Ku tuna cewa fusatattun ma’aikatan, a mako biyu da suka gabata sun rufe majalisar dokoki, inda suka hana yan majalisa zama, sannan suka nemi a tsige magatakardan majalisar dokokin, Alhaji Sani Omolori.

Koda dai fusatattun ma’aikatan sun hana sauran mutane dake kasuwanci irin yan jarida, bankuna, masu sayar da abinci da sauransu shiga harabar majalisar, amma da misalin karfe 10:30 sun ba kowa damar shiga majalisar.

KU KARANTA KUMA: Mambobin APC 5,000 sun sauya sheka zuwa PDP a jihar Ondo

Sai dai kuma rashin wutar lantarki da wuta a majalisar ya tursasa yan majalisar da sauran ma’aikatan da suka sam damar shiga ofishinsu gaggawar barin majalisar zwaa gidajensu. Ko ina yayi duhu sannan na’urar dake Dakar mutane zuwa sama suka daina aiki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel