Kaso 90 na yan Najeriya sun yanke shawarar zabar Atiku - Fayose

Kaso 90 na yan Najeriya sun yanke shawarar zabar Atiku - Fayose

- Tsohon gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose a ranar Litinin ya bayyana cewa Shugaba Buhari ya rasa dukkanin wani kyakyawar dama na yin tazarce cewa lokaci yayi da zai bar kujerar mulki

- Fayose yayi ikirarin cewa kaso 90 na ýan Najeriya sun yanke shawarar zabar Atiku

- Yayi zargin cewa jam’iyya mai mulki da Buhari na shirin yin magudin zaben 2019 yayinda ya shawarci yan Najeriya da su lalata wannan shiri

Wani tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose a ranar Litinin, 17 ga watan Disamba ya bayyana cewa dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Muhammadu Buhari ya rasa dukkanin wani kyakyawar dama na yin tazarce cewa lokaci yayi da zai bar kujerar mulki.

Fayose ya bayyana hakan a wani sakon fatan alkhairi a wani taro da aka shirya don dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar a Lagas a ci gaba da kamfen dinsa da ke gudana don zaben 2019.

Yayi ikirarin cewa kaso 90 na ýan Najeriya sun yanke shawarar zabar Atiku.

Kaso 90 na yan Najeriya sun yanke shawarar zabar Atiku - Fayose

Kaso 90 na yan Najeriya sun yanke shawarar zabar Atiku - Fayose
Source: UGC

A cewarsa, hakan ya isa bayanin dalilin da yasa APC ba za ta iya fita domin yin kamfen a saboda babu abunda zata nuna wa yan Najeriya cewar sun cimma nasara a shekaru uku da suka gabata.

KU KARANTA KUMA: Mambobin APC 5,000 sun sauya sheka zuwa PDP a jihar Ondo

Yayi zargin cewa jam’iyya mai mulki da Buhari na shirin yin magudin zaben 2019 yayinda ya shawarci yan Najeriya da su lalata wannan shiri.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel