Akwai alamun rashin gaskiya a tsarin habaka kasuwanci na TraderMoni – Bincike

Akwai alamun rashin gaskiya a tsarin habaka kasuwanci na TraderMoni – Bincike

Jaridar Punch tayi wani dogon bincike inda ta gano cewa akwai ta-cewa a tsarin nan na TraderMoni da Gwamnatin Shugaba Buhari ta kawo domin agazawa kananan ‘Yan kasuwa a cikin Jihohin Najeriya.

Akwai alamun rashin gaskiya a tsarin habaka kasuwanci na TraderMoni – Bincike

Jami'an TraderMoni su na zaftare bashin da ake ba 'Yan kasuwa
Source: Twitter

Wani ‘Dan kasuwa a Legas mai suna Mike Daramola, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta aiko masa N8000 ne a maimakon N10000 da aka yi masa alkawari. Duk da haka kuma ana sa rai ya biya bashin N10000 a shekara mai zuwa.

Gwamnati za ta rika bada bashin kudi daga N10,000, har zuwa N15,000, N20,000 zuwa ma N50,000 ga ‘Yan kasuwa. Idan mutum ya biya bashin da ke kan sa a cikin watanni 6, sai a kara masa wasu kudin domin ya cigaba da juyawa.

Daramola wanda yake da shago a kasuwar Sabo da ke Garin Ikorodu ya jawo hankalin Hukuma bayan an zaftare N2000 daga cikin kudin da ake badawa.

Ga abin da Daramola ya rubuta a shafin Tuwita da Ingilishi:

“So I received the #TraderMoni by #FG today, but to my surprise, the officials gave out N8,000 instead of N10,000 which means they deducted N2,000 each from everyone who got the money. How do we make Nigeria work with such acts? @DrJoeAbah, @ProfOsinbajo, @segalink, @feladurotoye.”

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari ta fara rabawa ‘Yan Najeriya kudin TraderMoni

Kamar yadda mu ka samu labari, akwai mutane da-dama da aka zaftarewa N2000 daga cikin bashin ba tare da bada wani dalili ba, inda kuma ake tsammani su biya N10, 000 bayan wani 'dan lokaci. Da alama dai wasu ne ke yin gaba da kudin.

Wani Bawan Allah a kasuwar ta Sabo ya bayyanawa ‘Yan Jarida cewa shi ma N8000 aka ba shi a maimakon N10000. Wannan ya sa wasu su ke ganin cewa kyauta ce kurum Gwamnatin Buhari ta ke badawa ba wai bashin kasuwanci ba.

Shi kuma wani cewa yayi, yana zaune kurum Jami’an Gwamnati su ka tambayi lambar wayar sa, kwatsam sai aka ce masa za a ba shi kudi ya saka a jarin sa, nan take kuwa yace a kawo tun da a ganin banza ne kurum ya samu ba komai ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit Newspaper

Online view pixel