Majalisa na bakin kokari wajen ganin ba ayi wahalar mai ba – Sanata Marafa

Majalisa na bakin kokari wajen ganin ba ayi wahalar mai ba – Sanata Marafa

Mun ji cewa a karshen makon nan ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gana da wasu manyan ‘Yan Majalisar Dattawa domin ganin ba ayi fama da wahalar man fetur a cikin karshen shekarar nan ba.

Majalisa na bakin kokari wajen ganin ba ayi wahalar mai ba – Sanata Marafa

Marafa ya gana da Shugaba Buhari wanda shi ne Ministan mai
Source: Twitter

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa, Shugaban kwamitin nan na harkar man fetur a Majalisar Dattawa watau Sanata Kabiru Marafa ya gana Shugaban Kasa. An yi wannan ganawa ne a karshen makon nan a cikin fadar Shugaban kasa na Villa.

Babban Sanatan na Jam’iyyar APC mai mulki ya zanta da ‘Yan Jaridar da ke Aso Villa game da batun wahalar mai, bayan ya zanta da Shugaban kasa inda ya bayyana cewa Najeriya na da isasshen man fetur da zai kai tsawon rabin shekara.

KU KARANTA:

‘Dan Majalisar na Jihar Zamfara ya bayyana cewa inda matsalar ta ke shi ne wajen biyan ‘yan kasuwa kudin tallafin man fetur da kuma sarkakiyar canjin Dala da kuma riba. Sanatan yace yana sa rai za a shawo kana wadannan matsala.

Sanatan yace sun ji shiru daga bangaren babban banki na CBN da kuma ofishin DMO don haka dole ya zanta da Shugaban kasa domin gudun a samu matsala a daidai lokacin da ake bukukuwan Kirismeti da kuma sabuwar shekara a kasar.

Marafa yace a makon gobe Majalisa za ta zauna da duk wani mai hannu a harkar man fetur domin ganin yadda za a magance duk wata matsala. Sanatan ya nuna cewa Buhari ya gaji wasu matsaloli a Gwamnati ne bayan hawan sa mulki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel