Gwamnati ta bari ‘Daliban Najeriya da ke karatu a Turai sun shiga halin ha’ula’i

Gwamnati ta bari ‘Daliban Najeriya da ke karatu a Turai sun shiga halin ha’ula’i

- Wadanda aka tura karatu zuwa Kasar Rasha su na wayyo Allah

- Gwamnatin Najeriya ta daina aikawa ‘Daliban na ta kudin cefane

Gwamnati ta bari ‘Daliban Najeriya da ke karatu a Turai sun shiga halin ha’ula’i

‘Yan Najeriya da aka tura Makaranta a waje su na kuka
Source: Twitter

‘Yan Najeriya da Gwamnatin Tarayya ta tura karatu a Kasar Rasha su na cikin wani mawuyacin hali kamar yadda mu ka samu labari. Yanzu haka wadannan Bayin Allah sun aikowa Shugaban kasa Buhari wasika ta musamman.

Gwamnatin Najeriya ta kan aika Yara masu hasaka zuwa Kasashen ketare irin su Rasha, Turkiyya, Sin, Maroko, Romaniya, Sabiya, Siriya, Kuba, Misra, da Kasar su Girka da sauran su domin yin Digiri ko kuma Digirgir da Digir-Digir.

Sai dai yanzu wadanda aka tura ketaren daga Najeriya ta wannan tsari na BEA su na fuskantar wahalhalun rayuwa iri-iri. A ka’idar yarjejeniyar ta BEA, Kasashen wajen ke biyan kudin makarantar ‘Yan Najeriyan da ke kasar.

Gwamnatin Najeriya kuma ta kan aikawa Mutanen na ta kudi akalla $500 a kowane wata domin samun na kashewa. Sai dai abin takaici shi ne, yanzu Gwamnatin Kasar tayi watsi da kudin cefanen da ta saba turawa ‘Daliban na ta a duk wata.

KU KARANTA: Masu cin gajiyar shirin N-Power sun yi zanga-zanga a Kaduna

Kasashen na ketare dai ba su taba sabawa alkawarin da su kayi ba, sai dai Gwamnatin Najeriya ta gaza cika na ta. Abin takaicin kuma shi ne ana cigaba da turo wasu ‘Daliban yayin da ake bin Gwamnati bashin kusan $1400 kawo yanzu.

‘Daliban da ke karatun Digiri na 2 da na 3 kuwa a Kasar Rasha su na bin Gwamnati bashin abin da ya kai $2500 zuwa $11606. Iyayen yara ne dai ke kokari wajen tura masu na kashewa a dalilin sakacin Gwamnatin Kasar na tsawon lokaci.

Lawan Mustapha wanda shi ne Shugaban ‘Daliban Najeriya da ke karatu a Kasar Rasha ya aikawa Shugaban Kasa Buhari da kuma Mataimakin sa, Yemi Osinbajo da sauran Ministocin Najeriya wasika domin su kawo masu daukin gaggawa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel