2018: Mun saka jarin $100m a Nigeria - Gwamnatin kasar Sin

2018: Mun saka jarin $100m a Nigeria - Gwamnatin kasar Sin

- Gwamnatin kasar Sin (China) ta ce kamfanoni mallakin kasar sun saka hannun jarin da ya kai na $100m a cikin watanni 10 na farkon shekarar 2018

- Haka zalika gwamnatin Sin, ta jaddada yunkurinta na baiwa Nigeria fifiko wajen harkokin kasuwanci da saka jari, don farfado da masana'antun kasar

- Sin ta kara da cewa kasashen guda biyu sun kasance masu riko da martabar juna da kuma kara karfafa dangantakarsu ta shige da ficen kayayyaki a fannin cinikayya

Gwamnatin kasar Sin (China) ta ce kamfanoni mallakin kasar sun saka hannun jarin da ya kai na $100m a cikin watanni 10 na farkon shekarar 2018.

Haka zalika gwamnatin Sin, ta jaddada yunkurinta na baiwa Nigeria fifiko wajen harkokin kasuwanci da saka jari, wanda zai taimaka ainun wajen farfado da masana'antu da kuma daga daga darajar fannin noma na kasar.

Babban jami'in tattalin arziki da kasuwanci na kasar Sin, a ofishin jakadancin kasar Sin a Abuja, Mr Zhao Linxiang, ya bayyana hakan a wani bukin lifya da aka shiryawa masu cin gajiyar wani shirin horo da ake gudanarwa a birnin Sin.

KARANTA WANNAN: Bamu da niyyar kawo tsaiko a yaki da ta'addanci - Martanin Amnesty International ga rundunar soji

2018: Mun saka jarin $100m a Nigeria - Gwamnatin kasar Sin

2018: Mun saka jarin $100m a Nigeria - Gwamnatin kasar Sin
Source: Facebook

Ya ce bayan ziyarar shugaban kasa Muhammadu Buhari zuwa Sin a 2016, kasashen guda biyu suka kasance suna aiki kafada da kafada da juna don a gudu tare a tsira tare, tare da kuma cimma muradi daya na bunkasa tattalin arzikin kasashen biyu.

Linxiang ya kara da cewa kasashen guda biyu sun kasance masu riko da martabar juna da kuma kara karfafa dangantakarsu ta shige da ficen kayayyaki a fannin cinikayya, musamman ma na yin kasuwanci da kudaden kasashen ckin farashi mai sauki.

Ya tariyo ziyarar shugaban kasa Buhari zuwa China a watan Satumba 2018, inda ya halarci taron bunkasa alaka tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika (FOCAC) da ya gudana a Beijing, inda shugaban kasa Buhari da shugaban kasar Sin, Xi Jinping, suka gudanar da wata ganawa ta musamman don samar da hanyoyin bunkasa hadin guiwa a tsakaninsu.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel