Bamu da niyyar kawo tsaiko a yaki da ta'addanci - Martanin Amnesty International ga rundunar soji

Bamu da niyyar kawo tsaiko a yaki da ta'addanci - Martanin Amnesty International ga rundunar soji

- Kungiyar kare hakkin bil Adama, Amnesty International, ta karyata ikirarin rundunar sojin Nigeria na cewar tana son kawo cikas a yaki da ta'addanci a Nigeria

- Amnesty International ta ce wannan zargin da barazanar da rundunar soji ke yi na dakatar da aikin kungiyar ba shi ne zai kawo karshen kashe kashen da ake yi ba

- Haka zalika Amnesty International ta ce ita dai tana kokarin ganin jigogin kasar sun hada kansu waje daya don kawo karshen kisan gillar da ake yiwa 'yan Nigeria

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta kasa da kasa, Amnesty International, ta karyata ikirarin da rundunar sojin Nigeria ta yi na zargin kungiyar da yi mata kutse cikin aiki tare da shiga hancinta da kudundune a yunkurin kawo karshen ta'addancin da ke faruwa a fadjn kasar.

Shugaban kungiyar Amnesty International na Nigeria, Auwal Rafsanjani, ya bayyana matsayar kungiyar a ranar Litinin a lokacin gabatar da rahotonta mai taken: "Girbe Mutuwa: Shekaru uku na rikici tsakanin Manoma da Makiyaya", a otel din Continental, Abuja.

"Martani na ga wannan ikirari na rundunar soji da kuma yunkurinta na rufe kungiyar Amnesty International ko wasu kungiyoyin da ke kare hakkin bil Adama da ke aiki a Nigeria, shine, hakan ba shi ne zai kawo karshen tauye hakkin dan Adam a kasar ba, kuma ba shi zai magance matsalolin tsaron kasar ba," a cewar Mr Rafsanjani.

KARANTA WANNAN: Gwamnatin tarayya ta haramtawa Ekweremadu, Bafarawa, da wasu mutane 27 fita kasashen waje

Bamu da niyyar kawo tsaiko a yaki da ta'addanci - Martanin Amnesty International ga rundunar soji

Bamu da niyyar kawo tsaiko a yaki da ta'addanci - Martanin Amnesty International ga rundunar soji
Source: Depositphotos

Ya jaddada cewa ko kadan kungiyarsu bata da wani mummunan nufi ga kowa, hasalima kungiyar bata da hannu a harkokin siyasa ko kuma lalata rayuwar wani, don haka bai kamata a zargeta da son kawo cikas ga yunkurin magance matsalolin tsaro a kasar ba.

"Yancinka da za a iya kare maka shi yau, har ila yau shine dai za a iya tauye maka shi gobe kuma idan har baka da muryar da zaka iya yin magana a madadin marasa katabus, to kuwa an samu babbar matsala."

Idan ba a manta ba, a ranar Litinin, mai magana da yawun rundunar soji, Sani Usman, a cikin wata sanarwa ya zargi kungiyar Amnesty International da daukar nauyin wasu kungiyoyi na yin zanga zanga, da kuma yiwa wasu shuwagabannin rundunar kazafi.

Sai dai Mr Rafsanjani ya ce Amnesty International na kokarin ganin jigogin kasar sun hada kansu waje daya don kawo karshen kisan gillar da ake yiwa 'yan Nigeria.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel