Watanni 5 babu albashi: Masu cin gajiyar shirin N-Power sun gudanar da zanga-zanga a Kaduna

Watanni 5 babu albashi: Masu cin gajiyar shirin N-Power sun gudanar da zanga-zanga a Kaduna

- Masu cin gajiyar shirin N-Power a jihar Kaduna, sun gudanar da zanga zanga, sakamakon hana su albashinsu na tsawon watanni biyar

- An dauke su aikin ne a watan Nuwambar 2018, sai dai tun bayan tantance su a watan Ogusta, basu sake samun albashinsu ba, duk da cewar suna zuwa aiki

- Sun roki gwamnatin jihar Kaduna da ta share masu hawayensu ta hanyar biyansu hakkokinsu kasancewar da yawansu na da iyalan da suke kula da su

A ranar Litinin, masu cin gajiyar shirin N-Power sun yin dafifi zuwa ma'aikatar kula da kananan hukumomin jihar Kaduna sakamakon rashin biyansu albashi har na tsawon watanni biyar, tun daga shekarar 2017.

Masu cin gajiyar shirin, sun koka kan yadda gwamnatin jihar Kaduna ta mayar da su wofi wajen biyansu hakkokinsu kamar yadda yake kunshe a cikin yarjejeniyar aikin.

Da yake jawabi a madadin masu gudanar da zanga zangar, Abubakar Aliyu, wanda ya ce an dauke su aiki cikin shirin ne a watan Nuwambar 2017, ya bayyana cewa tun bayan tabbatar da su a watan Ogusta 2018, babu wani albashin da aka biyasu.

KARANTA WANNAN: Zargin cin hanci: Duba tambayoyi 10 da Atiku ya yiwa Buhari

Watanni 5 babu albashi: Masu cin gajiyar shirin N-Power sun gudanar da zanga-zanga a Kaduna

Watanni 5 babu albashi: Masu cin gajiyar shirin N-Power sun gudanar da zanga-zanga a Kaduna
Source: Depositphotos

Aliyu ya yi zargin cewa wasu daga cikinsu da ke da uwa a gindin murhu a cikin gwamnatin sun samu albashinsu na watan Nuwamba kacal, ba tare da biyan sauran ba.

"Kafin yanzu, an kira matasa 'malalata', amma yanzu mun zage damtse muna aiki na tsawon lokaci ba tare da an biyamu hakkokinmu ba tun na watan Augusta. Da yawanmu na da iyalai da suke jiran tallafinmu, amma mai makon mu samu kudi daga aikin da muke yi, sai dai labarin ya canja kansa, domin kuwa muke kashe kudadenmu wajen zirga zirga zuwa wajajen da muke aiki, kuma tsawon watanni biyar kenan basu biyamu ba."

Don haka sai ya bukaci gwamnatin jihar Kaduna da ta duba wannan kuka nasu tare da share masu hawayensu ta hanyar biyansu basussukan da suke bin gwamnatin.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel