Barazana ga demokradiyya: Ku sa ido a kan Shehu Sani, Danjuma ya gargadi hukumomin tsaro

Barazana ga demokradiyya: Ku sa ido a kan Shehu Sani, Danjuma ya gargadi hukumomin tsaro

Cibiyar dattawa na kasa tayi kira ga hukumomin tsaro su sanya idanu a kan dan majalisar jihar Kaduna mai wakiltan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani wadda suka ce ya zama kware wajen tunzura mutane domin tayar da zaune tsaye.

Shugaban cibiyar, Elder Anthony Danjuma wanda ya yi wannan furucin a ranar Litinin a Kaduna ya bayyana damuwarsa kan yadda rashin daukar matakin hukunci a kan Shehu Sani ke bashi kwarin gwiwar cigaba da tunzura mutane a Kaduna.

Danjuma ya yi gargadin cewa rashin sanya ido a kan Shehu Sani yana nufin yiwuwar afkuwar fitintinu duba da yadda akwai hujoji da yawa daga shafinsa na sada zumunta da ke nuna cewa yana kokarin kawo tangarda da demokradiyyar Najeriya.

Barazana ga demokradiyya: Ku sa ido a kan Shehu Sani, Danjuma ya gargadi hukumomin tsaro

Barazana ga demokradiyya: Ku sa ido a kan Shehu Sani, Danjuma ya gargadi hukumomin tsaro
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Cikaken jerin sunayen mambobin majalisar wakilai da ba za su koma majalisar ba a 2019

Dattijon ya bayyana damuwarsa kan yadda Sanatan na Kaduna ke amfani da damar da ya ke dashi a matsayin sanatan Najeriya wurin yadda kalaman kiyaya wadda idan da a wasu kasashen ne da tuni an aike dashi gidan yari.

Danjuma ya ce, "Bamu san dalilin da yasa hukumomin tsaro za su jira har sai dattawa sunyi magana ba kafin su sa ido a kan mutanen da ke kokarin tayar da fitina a kasar a yayin da suke nuna wa kamar suna kishin kasa ne. Idan da tsohuwar jam'iyyarsa ba ta nisanta kansa daga shi ba, da yanzu baya irin wannan abubuwan da ya keyi.

"Abinda muke tsamani shine hukumomin tsaro su gayyace shi ya fada musu yadda ya gano cewa ba za ayi adalci ba a babban zaben 2019 tunda a yanzu babu wani hujja da ta nuna cewa hukumar zabe ba za tayi adalci ba.

"Ya kamata hukumomin tsaro su sani cewa dole ne dokar da ke aiki a kan wasu 'yan Najeriya a yayin da suka furta kalaman tayar da hankali tayi aiki a kan Shehu Sani.," inji Danjuma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel