Zan basu damar da suka hana ni - Buhari ya yiwa PDP albishir

Zan basu damar da suka hana ni - Buhari ya yiwa PDP albishir

A yau, Litinin, ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi alkawarin cewar gwamnatinsa zata bawa dukkan 'yan takara a zaben shekarar 2019 dama domin gwada farinjininsu ba tare da tsangwama ko muzgunawa ba.

Buhari ya fadi hakan ne yayin karbar bakuncin wasu mambobin cibiyar siyasar kasar Amurka a fadar sa dake Abuja.

"Na ji dadin ziyarar ku domin ganin yadda muke shirye-shiryen gudanar da zabukan shekarar 2019," a cewar Buhari ta bakin kakakinsa, Femi Adesina.

"Ziyarar ku ta tuna min da ziyarar da Johb Kerry, sakataren gwamnatin kasar Amurka na wancan, ya kawo Najeriya gabanin zabukan shekarar 2015. Muna godiya da irin kulawa da damuwa da ku ke nunawa a kan jaririyar siyasar Najeriya," a kalaman Buhari.

Sannan ya cigaba da cewa, "a matsayina na wanda ya yi takara sau uku amma yana karewa a kotu, kafin daga bisani fasahar zamani da taimakon Allah su kai ni fa nasara, ba zan bari a yiwa wani magudin zabe ba saboda na san bakincikin da yin hakan ke haifarwa.

Zan basu damar da suka hana ni - Buhari ya yiwa PDP albishir

Buhari
Source: Twitter

"Abinda suke yi a wancan lokacin shine su raba kuri'u ga 'yan takarar da suke so, sannan su fadawa 'yan takarar da suka yiwa magudi cewar su tafi kotu. Amma ni ba zan yi masu haka ba, zan bawa jam'iyyar adawa damar da basu bani ba a wancan lokacin."

DUBA WANNAN: Duk kanzon kurege ne, bani da niyyar barin PDP - Kwankwaso

Buhari ya shaidawa bakin nasa cewar ya umarci shugabannin hukumomin tsaro da su yi aikinsu bisa gaskiya, ba tare da nuna fifiko ga wani dan takara ko wata jam'iyya ba.

Kazalika ya bayyana cewar jam'iyyar APC zata yi yakin zabe ne a kan abubuwa da tayi kamfen dasu a shekarar 2015; yaki da cin hanci, tabbatar da tsaro, da inganta tattalin arzikin kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel