Da dumin sa: An tashi baram-baram a taron tattauna mafita tsakanin ASUU da gwamnati

Da dumin sa: An tashi baram-baram a taron tattauna mafita tsakanin ASUU da gwamnati

Yanzu haka labarin da muke samu na tabbatar mana da ne da cewa an tashi baram-baram a taron tattauna mafita tsakanin shugabannin kungiyar malaman jami'o'i na Najeriya watau Academic Staff Union of Universities (ASUU) a turance da kuma jami'an gwamnati domin tattaunawa akan yajin aikin da yanzu haka suke yi.

Majiyar mu dai ta bayyana mana cewa an ga shugabannin kungiyar sun fito daga dakin taron da suke cikin yi da jami'an gwamnatin a ma'aikatar ilimi ba tare da yiwa 'yan jarida bayani ba sannan kuma suka shige motocin su suka tafi.

Kamar yadda muka samu, shugaban kungiyar ta Academic Staff Union of Universities (ASUU) Biodun Ogunyemi ne ya jagoranci shugabannin kungiyar wadanda aka gani a ma'aikatar Ilimi ta gwamnatin tarayya a garin Abuja tun wajen karfe 5 na yamma.

Da dumin sa: An tashi baram-baram a taron tattauna mafita tsakanin ASUU da gwamnati

Da dumin sa: An tashi baram-baram a taron tattauna mafita tsakanin ASUU da gwamnati
Source: UGC

KU KARANTA: Uwar mu daya da Buhari - Atiku

Legit.ng Hausa ta samu haka zalika cewa su kuma jami'an gwamnati sun samu jagorancin ministan kwadago ne watau Chris Ngige wanda ya iso a ma'aikatar da misalin karfe 6 na yamma kafin daga bisani su shiga tattaunawa.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa tun a ranar 4 ga watan Nuwamba ne kungiyar ta ASUU ta shiga yajin aiki na sai baba ta gani inda suke bukatar gwamnati ta kara zuba kudi a harkar ilimin kasar da kuma biyan su hakkokan su.

Kafin wannan ranar dai, bangarorin biyu sun tattauna akalla sau hudu akan yadda za'a cimma matsaya akan lamarin amma haka bata cimma ruwa ba har yanzu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel