Kididdigar yawan marasa aikin yi tsohuwa ce ba ta yanzu ba - Buhari

Kididdigar yawan marasa aikin yi tsohuwa ce ba ta yanzu ba - Buhari

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci NBS da ta canza kididdigarta ta fannin rashin aikin yi

- Ya bukace su dasu yi duba da irin samuwar aiyukan yi ta bangaren noma

- Mai magana da yawun kungiyar yakin neman zaben Atiku Abubakar ya zargi fadar shugaban kasar da yunkurin canza yawan marasa aikin yi ganin gabatowar zabe

Kididdigar yawan marasa aikin yi tsohuwa ce ba ta yanzu ba - Buhari

Kididdigar yawan marasa aikin yi tsohuwa ce ba ta yanzu ba - Buhari
Source: Twitter

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci shugaban NBS, Dr. Yemi Kale, da ya canza kididdigar su ta yawan marasa aikin yi tare da duba da yawan aikin yi da bangaren noma ya samar a kasar.

Babban mataimakin shugaban kasa na musamman ta bangaren yada labarai, Mallam Garba Shehu, ya sanar da hakan a wani shirin gidan talabijin na Channels, mai suna Sunrise Daily.

Shehu yace a wani taron kwanan nan da FEC, Kale yace NBS kawai duba take ga aiyukan da aka samar ta bangaren masu karatun boko ba wai bangaren noma ba.

DUBA WANNAN: Siyasar Yanki: Hanyoyi 10 da Rabi'u Kwankwaso zai iya koyar siyasa daga Malaminta Jagaba Bola Tinubu

Yace shugaban ya sanar dashi dasu hanzarta gyara kuskuren su tare da bayyanawa mutane.

"Kungiyar manoman shinkafa ta Najeriya ta fito ta bayyana yanda ta samar da aiyukan yi har miliyan 12,har yanzu kuma babu wanda ya fito ya kalubalance su."

Amma kuma mai magana da yawun kungiyar yakin neman zaben Atiku Abubakar, Mista Phrank Shuaibu, wanda shima yake a shirin, ya maida martani ga Shehu, inda ya zargi fadar shugaban kasar da yunkurin canza kididdigar don ganin gabatowar zabe.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa.

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel