Ministan matasa da zan nada ba zai haura shekara 30 ba - Atiku

Ministan matasa da zan nada ba zai haura shekara 30 ba - Atiku

- Atiku Abubakar ya ce ministan matasa da zai nada idan ya lashe zaben shugabancin kasa ba zai haura shekaru 30 ba

- Wazirin Adamawa ya yi wannan furuci ne a wurin wani taron jin ra'ayi da matasa da akayi a jihar Legas

- Atiku ya ce matasa sune manyan gobe kuma ya zama dole a fara janyo su ciki a gwamnati domin su samu kwarewa a aiki

Dan takarar shugabancin kasa karkashin inuwar jam'iyyar PDP kuma tsohon mataimakin kasar Najeriya, Atiku Abubakar ya ce idan ya lashe shugaban kasa, zai nada matashi wanda bai wuce shekaru 30 ba a matsayin ministan matasa.

Dan takarar na PDP ya yi wannan alkawarin ne a wurin wani taron jin ra'ayin al'umma da akayi a Legas a ranar Litinin.

Atiku ya bayyana irin wanda zai nada ministan matasa

Atiku ya bayyana irin wanda zai nada ministan matasa
Source: Facebook

A cewarsa, nauyi ya rataya ga shugabanin da ke mulki a yanzu su bawa matasa horon da ya dace kuma hanyar mafi ingancin yin hakan shine nada matasa masu hazaka a kan madafan iko na gwamnati domin su goge a harkar mulkin.

DUBA WANNAN: Cikaken jerin sunayen mambobin majalisar wakilai da ba za su koma majalisar ba a 2019

"Nayi alkawari cewa zan bawa matasa kashi 40 na mukamai a gwamnati na. Ina son in tabbatar muku cewa ba zan saba wannan alkawarin ba. Ministan matasa na ba zai kasance wanda bai wuce shekaru 30 a duniya ne ba."

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce zai baiwa fannin ilimi da muhimmanci idan aka zabe shi, ya ce "shugaba Buhari ya amince cewa tattalin arzikin Najeriya yana cikin mawuyacin halin hakan na nuna cewa shugaban kasar bai san yadda zai inganta tattalin arzikin kasar ba. Babu wani kwarare kan tattalin arziki a gwamnatinsa shi yasa muka shiga wannan halin.

"Na san yadda ake gyra tattalin arziki. Na san yadda ake kirkiran ayyuka kuma na san yadda ake tallafawa matasa. Wannan shine dalilun da yasa na zo nan a yau - domin in baku kwarin gwiwa cewar tare za mu iya gyra Najeriya," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel