Duk kanzon kurege ne, bani da niyyar barin PDP - Kwankwaso

Duk kanzon kurege ne, bani da niyyar barin PDP - Kwankwaso

Tsohon gwamna kuma Sanatan jihar Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso, ya yi watsi da rahotannin dake yawo a gari kan cewar yana shirin fita daga jam'iyyar PDP tare da komawa jam'iyyar PDP.

Da safiyar yau ne wasu kafafen yada labarai suka wallafa rahoton cewar gudun yin batan bakatantan ya sanya tsohon gwamna kuma Sanatan jihar Kano ta tsakiya, Rabi'u Musa Kwankwaso, ya aika wakilansa zuwa fadar shugaban kasa domin share masa hanyar dawowa jam'iyyar APC.

A watan Yuli na shekarar nan ne Sanata Kwankwaso tare da ragowar mambobin majalisar dattijai 12 suka canja sheka daga jam'iyyar APC zuwa PDP.

Tsohon gwamnan ya koma jam'iyyar PDP inda ya yi takarar neman zama dan takarar shugaban kasa amma ya kare a mataki na hudu. Wata majiyar ta ce hankalin Kwankwaso ya kasa kwanciya da yadda al'amuran siyasa ke tafiya a cikin jam'iyyar PDP.

Majiyar ta kara da cewar dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ki sakin ko sisi domin fara yi masa yakin neman zabe a Kano duk da Kwankwaso ya bashi kiyasin N1bn a matsayin kudin da suke bukata domin aiyuka da hidimar yi masa kamfen.

Duk kanzon kurege ne, bani da niyyar barin PDP

Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso
Source: Twitter

Kamar yadda majiyar ta sanar, ta ce tun bayan da Kwankwaso ya mika bukatar adadin kudin, Atiku ya yi burus da maganar duk da Kwankwason ya yi masa tuni ba sau daya ba.

Kazalika, majiyar ta ce Kwankwaso ya ji ciwon yadda Atiku ya ki nada shi jagorancin yakin neman zabensa a yankin arewa maso yamma.

Wani lamari da majiyar ta ce ke kara tayar wa da Kwankwaso hankali shine yadda jiga-jigan tafiyar Kwankwasiyya ke nuna rashin jin dadinsu bisa tsayar da surukinsa, Abba Kabir Yusif, a matsayin dan takarar gwamnan jihar Kano a jam'iyyar PDP.

DUBA WANNAN: Aiyukan da gwamnatin Buhari ke yi a jihohin arewa maso yamma

Majiyar ta ce a yanzu haka wasu manyan yaran tsohon gwamnan da suka hada da shugaban jam'iyyar PDP kuma tsohon sakataren gwamnatin jihar Kano, Rabi'u Suleiman Bichi; tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, Farfesa Hafizu Abubakar; Alhaji Bala Gwagwarwa, da sauransu na kan hanyar komawa jam'iyyar APC.

Sai dai a jawabin da Kwankwaso ya fitar a shafinsa na Tuwita ya ce, "ana yada wani labarin kanzon kurege a dandalin sada zumunta cewar zan fita daga jam'iyyar PDP. Ina mai yin watsi da wannan labarin karya tare da kara jaddada cewar ni dan PDP ne kuma bani da niyyar fita daga jam'iyyar; a yanzu ko wani lokaci a nan gaba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel