Jihar Legas: PDP zata samu nasara kan APC da tazarar kuri'u masu yawa - Agbaje

Jihar Legas: PDP zata samu nasara kan APC da tazarar kuri'u masu yawa - Agbaje

- Dan takarar gwamnan jihar Legas karkashin jam'iyyar PDP, Mr Jimi Agbaje, ya ce idan zaben 2019 yazo, jam'iyyar zata lallasa APC da kuri'u masu tazara

- Agbaje ya kuma zargi APC a jihar na cewar tana bin duk wasu hanyoyi na dakile yakin zabensa a jihar da kuma kawo cikas a wajen zaben gwamnan jihar na matan Maris, 2019

- Agbaje, wanda ya yi jawabinsa da turancin 'broken', ya jaddadawa Alhaji Atiku Abubakar cewar PDP ce zata samu nasara don kawo karshen mulkin uban gida a jihar

Dan takarar gwamnan jihar Legas karkashin jam'iyyar PDP, Mr Jimi Agbaje, ya ce idan zaben 2019 yazo, jam'iyyar zata lallasa APC da kuri'u masu tazara, yana mai jaddada cewa kowacce al'umma a jihar Legas sun gaji da irin wannan mulkin kama karba na mutum daya.

Agbaje ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da jawabi a wani taron jin ra'ayoyin jama'a wanda aka shirya don kardafa yakin zaben dan takarar shugaban kasa na PDP, Alhaji Atiku Abubakar, wanda ya kai ziyarar yakin zabe a jihar Legas.

Wannan kuma ya biyo bayan zargin da dan takarar gwamnan jihar Legas karkashin jam'iyyar PDP ya yiwa APC na cewar tana bin duk wasu hanyoyi na dakile yakin zabensa a jihar da kuma kawo cikas a wajen zaben gwamnan jihar na matan Maris, 2019.

KARANTA WANNAN: Sakamakon kashe wata mata: Rundunar yan sanda ta cafke manaja da ma'aikatan wani otel

Jihar Legas: PDP zata samu nasara kan APC da tazarar kuri'u masu yawa - Agbaje

Jihar Legas: PDP zata samu nasara kan APC da tazarar kuri'u masu yawa - Agbaje
Source: Depositphotos

Agbaje, wanda ya yi jawabinsa da turancin 'broken', ya jaddadawa dan takarar shugaban kasar, Alhaji Atiku Abubakar cewar PDP ce zata samu nasara, yana mai cewa yin hakan ne kadai zai cire Legas daga hannun maha'inta da kuma kawo karshen mulkin ubangida a jihar.

"Mun dade muna wannan gwagwarmayar kuma ina mai tabbatar maka cewa wannan yakin zaben namu muna yinsa ne don 'yantar da jihar Legas daga kangin bauta. Muna fatali da irin wannan mulki na kama karba na uban gida," a cewar sa.

"Hanya daya da APC za ta iya samun nasara a yanzu shine magudi da aringizon zabe," yana mai ikirarin cewa jam'iyya mai mulki ta jihar na ci gaba da hango faduwa karara don haka ne ma ta dauki damarar lalata kayan yakin zaben PDP a jihar."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel