Sakamakon kashe wata mata: Rundunar yan sanda ta cafke manaja da ma'aikatan wani otel

Sakamakon kashe wata mata: Rundunar yan sanda ta cafke manaja da ma'aikatan wani otel

- Rundunar yan sanda ta cafke wani manajan otel da ma'aikatanss a Ebonyi

- An cafke ma'aikatan otel din ne biyo bayan mutuwar wata mata a cikin dakinta a ranar Lahadi, 16 ga watan Disamba

- Rahotanni sun bayyana cewa an tsinci gawar matar a cikin dakin tare da rauni mai zurfi a kirjinta da kumatunta

Rundunar 'yan sanda a Ebonyi na ci gaba da gudanar da bincike kan mutuwar wata mata da har yanzu ba a bayyana sunanta ko kuma wacece ba, wacce ta mutu a cikin dakin wani otel da ke kan titin Afikpo, Abakalili.

DSP Loveth Odaa, jami'ar hulda da jama'a ta rundunar 'yan sandan jihar, ta shaidawa manema labarai a Abakaliki, a ranar Lahadi, 16 ga watan Disamba, cewar wacce aka kashen, tana dauke da raunuka masu zurfi a kirjinta da kumatunta.

Odaa ta ce rundunar ta cafke manaja da kuma ma'aikatan otel din don gudanar da bincike akan kisan matar ta hanyar tuhumarsu.

KARANTA WANNAN: Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya cika shekaru 76 a duniya, kalli wankan da ya sha a yau (Bidiyo)

Sakamakon kashe wata mata: Rundunar yan sanda ta cafke manaja da ma'aikatan wani otel

Sakamakon kashe wata mata: Rundunar yan sanda ta cafke manaja da ma'aikatan wani otel
Source: Depositphotos

Ta kuma roki daukacin jama'ar jihar da su baiwa rundunar duk wasu muhimman jawabai da zasu taimaka wajen gano wanda ya kashe matar, kasancewar an gano gawar matar ne bayan yan kwanaki da kashe ta.

Wata majiya da ta bayyana a sakaya sunanta, ta bayyana cewar ma'aikatan otel din sun san ankara da mutuwar matar ne a lokacin da wari ya fara fitowa daga dakin nata.

"A lokacin da warin ya wuce kima, sai na sanar da hukumar otel din wadanda suka duba dakin tare da gano gawar matar kwance da raunuka a jikinta. Akwai zargin cewa saurayinta ya yayyanketa da wuka, bayan da hukumar otel din suka sanar da rundunar 'yan sanda."

Emmanuel Eze, manajar otel din, ya ce yayi tafiya a lokacin da lamarin ya faru, amma a sa'ilin da aka sanar da shi, ya hanzarta sanar da hukumar 'yan sanda.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel