Rikicin Manoma da makiyaya yayi sanadiyyar mutane 3600 daga 2016 zuwa 2018

Rikicin Manoma da makiyaya yayi sanadiyyar mutane 3600 daga 2016 zuwa 2018

Kungiyar nan ta Amnesty International ta yi wani bincike inda ta bayyana yawan wadanda aka hallaka a Najeriya ta sanadin rikicin da ya rika barkewa tsakanin Makiyaya da kuma Manoma a fadin Kasar nan.

Rikicin Manoma da makiyaya yayi sanadiyyar mutane 3600 daga 2016 zuwa 2018

Mutum 3600 aka kashe a sanadiyyar rikicin Makiyaya
Source: Depositphotos

Amnesty International ta fitar da rahoto cewa mutane akalla 3, 641 aka kashe a cikin shekaru 3 da su ka wuce a Najeriya. Binciken da Kungiyar tayi ya nuna cewa kusan kashi 57% na kashe-kashen da aka yi sun auku ne a shekarar nan.

Osai Ojigho, wanda shi ne babban Darektan Amnesty International a Najeriya ya bayyana yadda Makiyayan su ke kai manyan hare-hare a Kasar da mugayen makamai irin su bindigar AK-47 da bindigar nan mai uwar-watsi.

A cewar Kungiyar, hare-haren sun fara kamari ne a farkon 2016. Daga 2016 zuwa 2018, an kai hari fiye 300 a Jihohin da su ka hada da Adamawa, Benuwai, Kaduna, Taraba da Filato. Jami’an tsaro ne dai kuma su kan yi sake.

KU KARANTA: Mun yi nadamar zaben Buhari - Inji Matasan Arewa

Ojigho yace sun yi hira fiye da 260 a Kauyuka har 56 a wasu Jihohin Najeriya ban da tafiye-tafiye iri-iri domin gudanar da wannan bincike. Sauran Jihohin da Makiyayan kan yi barna sun hada da Ondo, Oyo, Delta, Enugu da Edo.

Inda rikicin ya fi kamari shi ne Taraba, Benuwai da kuma Jihohin Kaduna da Zamfara. A irin wadannan Yankuna, har ta kai Jami’an tsaro ba su iya yin komai idan har rikici ya barke tsakanin Makiyaya da kuma Manoma a Kasar.

Amnesty International ta fitar da wannan rahoto mai suna “Harvest of Death” yau a birnin Tarayya Abuja, hakan dai ya kawo rikici inda wasu su ka zargi Kungiyar da kokarin tada hankalin jama'a a Kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel