Hukumar kwastam ta samu amincewar shugaban kasa wajen raba kayayyakin da suka kwace ga yan gudun hijira da marayu

Hukumar kwastam ta samu amincewar shugaban kasa wajen raba kayayyakin da suka kwace ga yan gudun hijira da marayu

- Hukumar kwastam ta samu yardar shugaban kasa wajen rarraba kayayyakin da suka kwace ga sansanonin yan gudun hijira da gidajen marayu a fadin kasar

- Kakakin hukumar kwatam ne ya bayyana a lokacin wani taron cin abincin safe a Lagas

- Hukumar ta ce kusan rabin miliyan na shinkafa yar 50kg aka rarraba a yankin zuwa yanzu

Hukumar kwastam na Najeriya ta sam yardar shugaban kasa wajen rarraba kayayyakin da suka kwace ga sansanonin yan gudun hijira da gidajen marayu a fadin kasar.

Joseph Attah, kakakin hukumar kwatam ne ya bayyana a lokacin wani taron cin abincin safe a Lagas a ranar Litinin, 17 ga watan Disamba cewa kafin amincewar, ana rabon kayayyaki kamar su kayan sawa, shinkafa da man gyada ga sansanonin yan gudun hijira a yankin arewa maso gabas kawai.

Hukumar kwastam ta samu amincewar fadar shugaban kasa wajen kara kayayyakin da suka kwace ga yan gudun hijira da marayu

Hukumar kwastam ta samu amincewar fadar shugaban kasa wajen kara kayayyakin da suka kwace ga yan gudun hijira da marayu
Source: Depositphotos

Kusan rabin miliyan na shinkafa yar 50kg aka rarraba a yankin zuwa yanzu, inji hukumar.

Mista Attah yace tsakanin watan Janairu da Nuwamban wannan shekarar, hukumar kwastam ta biya naira triliyan 1.1 a asusun tarayya.

KU KARANTA KUMA: A yi hakuri da ni a kara min lokaci – Buhari

Yace an rigada an tanadi jerin sasanonin yan gudun hijira da gidajen marayun da za’a rarrabawa kayayyakin ba tare da bata lokaci ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel