Bayan watanni biyu: Manufarmu na canza suna zuwa Legit.ng Hausa - Mudathir Ishaq, Editan Jaridar Legit Hausa

Bayan watanni biyu: Manufarmu na canza suna zuwa Legit.ng Hausa - Mudathir Ishaq, Editan Jaridar Legit Hausa

Zuwa ga masu karatu: Sunana Mudathir Ishaq, babban Editan jaridar Legit.ng Hausa wacce a baya kuka sani da Naij.com Hausa ko Naija Hausa.

A watanni biyu da suka gabata, mun alantawa duniyar Hausa niyyar sauya suna zuwa Legit.ng Hausa bayan shekaru uku da bude wannan jaridar da ta buwaya kuma ta shahara a zauren labarai a duniyar jaridun Hausa.

KU KARANTA: Dawo da shafin Legit.ng akan manhajar Opera cikin hanyoyi uku

Manufarmu, ilmantar da al’ummar Hausa kan abubuwan da ke gudana yau da kullun

Manufarmu, amfanar da al’umma ta hanyar isar da koke-kokensu zuwa ga shuwagabanni

Manufarmu, tabbatar da cewa masu karatu na samun ingantattun labarai a koda yaushe

Manufarmu, kawo muku labarai ba tare da bata lokaci ba

Manufarmu, kawar da jabun labarai da ka iya sanya masu karatu cikin rudani da kuma haddasa sakamako mara dadi

Manufarmu, wayar da kan al’ummar Arewa kan harkokin siyasar gida da na waje

Manufarmu, yada al’adun Hausa musamman a zamani irin na yau da mutane suka fara mantawa da su

Manufarmu, Taimakawa mazauna karkara wajen sanin abubuwan da ke gudana a Najeriya cikin sauki

Manufarmu, baiwa matasa masu hazaka damar baja kolinsu wajen rubutun Hausa

Manufarmu, kara fadada buwayar harshen Hausa a fadin duniya

A Legit Hausa, ba’a binmu bashin bayanai, hujjoji, hotuna, bidiyoyi da majiyoyi masu inganci.

Ina fatan za ku ci gaba da kasancewa tare da mu a wannan sabuwar hanya da muka dauka.

Nan ba da dadewa ba, za ku samu damar tattaunawa kai tsaye da ni inda za ku iya bada gudunmuwarku, shawarwarinku da tambayoyi kan abubuwan da suka shige muku game da yadda muke gudanar da ayyukanmu.

Nagode.

Malam Mudathir Ishaq

Edita, Legit Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel