A yi hakuri da ni a kara min lokaci – Buhari

A yi hakuri da ni a kara min lokaci – Buhari

- Shugaba Buhari ya yi kira ga al’umman Najeriya da su ci gaba da hakuri da gwamnatin sa

- Ya ce su kara ba shi dan lokaci kadan domin ya samu damar isar da manufofin sa da shirin gwamnatin sa gare su

- A yau Litini 17 ga watan Disamba ne Shugaban kasar yaki bukin munar zagayowar ranar haihuwar sa

A daidai lokacin da cika shekaru 76 a duniya Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga al’umman Najeriya da su ci gaba da hakuri da gwamnatin sa sannan su kara ba shi dan lokaci kadan domin ya samu damar isar da manufofin sa da shirin gwamnatin sa gare su.

A yau Litini 17 ga watan Disamba ne Shugaban kasar yaki bukin munar zagayowar ranar haihuwar sa.

A yi hakuri da ni a kara min lokaci – Buhari

A yi hakuri da ni a kara min lokaci – Buhari
Source: UGC

A jawabinsa shugaban kasar ya jinjina wa ‘yan Najeriya sannan ya yi kira gare su da su ci gaba da hakuri da gwamnatin sa sannan a dan kara masa lokaci don ya samu ya isar da alkawuran da gwamnatin sa tayi wa jama’a

Bayan fareti da sojojin Najeriya suka yi wa shugaban kasa don karrama wannan rana Ministan tsaro, Mansur Dan-Ali, Shugaban ma’aikatan fadar shugaban Kasa, Abba Kyari duk sun mika wa shugaba Buhari Katin taya murna a madadin ma’aikatan fadar.

KU KARANTA KUMA: Cika shekaru 76: Wasu muhimman abubuwa 7 a kan Buhari

A wani lamari na daban, mun ji cewa wasu jam’iyyun siyasa guda goma sun sake hadewa da jam’iyyar Coalition of United Political Parties (CUPP) wadanda ke kokarin ganin sun tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari da jam’iyyarsa daga mulki a zaben 2019.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa wasu jam’iyyu siyasa kuma sun mika takardarsu na neman bin sahun masu adawa da gwamnatin APC.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel